Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Abubuwa biyar da Shugaban Najeriya Tinubu ya yi magana a kai a tattaunawarsa da manema labarai
Afrika

Abubuwa biyar da Shugaban Najeriya Tinubu ya yi magana a kai a tattaunawarsa da manema labarai

December 24, 2024
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn

A Ranar Litinin da ta gabata da maraice Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi tattaunawarsa ta farko da ‘yan jarida tun bayan da ya karɓi ragamar mulkin ƙasar a watan Mayun shekarar 2023.

A cikin tattaunawar da aka yada a gidan talabijin na ƙasar, shugaban ya amsa tambayoyi da dama ciki hadda abubuwan da suka fi ci wa ‘yan ƙasar tuwo a ƙwarya.

Cire tallafi man fetur da dala

Da aka tambaye shi game da yadda ya ji ganin irin tasirin da cire tallafin ya yi kan tattalin arzikin ƙasar, Shugaba Tinubu ya ce babu wata hanya da ƙasar za ta iya bi idan ba ta cire tallafi a lokacin da ya cire ba.

Cire tallafin man fetur da kuma dala dai ya haddasa ƙarin tsadar rayuwa a ƙasar. Sai dai kuma shugaban Nijeriya ya ce bai yi nadamar cire tallafin ba.

“Makomarmu muke lalatawa (da tallafin). Arzikin ‘ya’ya da jikokinmu muke kashewa. Ba ma zuba jari. Yaudarar kanmu kawai muke ta yi. Waɗannan gyare-gyaren sun zama dole,” in ji shugaban a lokacin da yake magana game da illar tallafin man fetur da dala.

Dokar Haraji

Da yake amsa tambaya kan dokar sake fasalin harajin ƙasa kuwa Shugaba Tinubu ya ce ya shirya domin tattaunawa da kuma yin sauye-sauye game da ababen da suka janyo ce-ce-ku-ce kan dokar musamman maganar harajin VAT.

Shugaban ya ce sake fasalin dokar na buƙatar tattaunawa da kuma yarjejeniya kuma shi ya shirya domin yin hakan.

Raba tallafi

Game da batun turmutsutsun da aka samu a wuraren raba tallafi a makon jiya inda fiye da mutum sittin suka mutu kuwa, Shugaba Tinubu cewa ya yi kurakuran waɗanda suka shirya ba da tallafin ne suka janyo turmutsutsun.

“Abin takaici ne mutane ba su tsara taron ba yadda ya kamata. Ya kamata mu kasance masu tsari a rayuwarmu. Ina miƙa saƙon ta’aziyya ga waɗanda suka rasa ‘yan’uwa, amma bayar da kyauta abu ne mai kyau,” in ji Tinubu.

Shugaban ya ce ya shafe shekara 25 yana ba da tallafi a gidansa da ke Legas ba tare da samun irin wannan matslar ba saboda tsari.

“Ko wace al’umma, ko Amerika ce, tana da wurin ba da abinci kyauta. Suna da mutane da ke jin yunwa. A Birtaniya, suna da wuraren ba da abinci da kuma wuraren adana abinci, kuma suna da tsari. Suna layi domin karɓar abinci,” in ji shi.

Tsadar gudanar da gwamnati

Da aka tambaye shi kan ko zai rage yawan ministocinsa domin rage tsadar gudanar da gwamnati, Shugaba Tinubu ya ce shi ba zai rage yawan ministocin nasa ba.

“Ban yi shirin rage yawan ministocina ba. Ni na san dalilin da ya sa na naɗa su. Ba na bai wa mutum aikin da na san ba zai iya yi ba,” in ji shi.

“Dole bayanin aiki ya zama cikakke da kuma ingantacce. Nijeriya ƙasa ce babba. Idan kana son ka ciyar da mutum fiye da miliyan 200, ka yi lissafin yawan ma’aikatan da za ka buƙata. Bari mu mayar da hankali kan inganci. Inganci shi ne abu mafi muhimmanci game da majalisar ministoci. Ina buƙatarsu,” a cewar shugaban.

Tsadar rayuwa

Da aka tambaye shi kan matakin da gwamnatinsa take ɗauka game da hauhawar farashin kayayyaki, shugaban ya ce: “kawai za mu ci gaba da ƙara yawan abubuwan da ake kai wa kasuwa ne. Za mu yi aiki tuƙuru domin ƙara yawan abubuwa da ake kai wa kasuwa.”

Da aka ƙara jan hankalin shugaban game da illar dillalai masu sayen abubuwa daga manoma domin cin riba, Shugaba Tinubu ya ce shi bai yarda da ƙayyade farashin kayayyaki ba, kuma ko ba jima ko ba daɗe idan aka ci gaba da ƙara yawan abubuwa da ake kai wa kasuwa dillalan za su faɗi.

“Alal misali, dubi farashin man fetur. Na samar da tsarin sayen ɗanyen mai da dala wanda ba su so bi ba. Sun yi jayayya da ni. Na ce to ku bari kasuwa ta yi halinta. Na bar shi. A yanzu farashin ya fara saukowa a hankali,” in ji shugaban.

Daga baya kuma shugaban ya sake magan kan tallafa wa manoma ta yadda za su ƙara yawan abincin da suke samarwa.

“Za mu sake bayar da ƙarin tallafi ga manoma, bashi mai sauƙin kuɗin ruwa, noman zamani mai amfani da injuna. Ba zai yiwu ba a koma irin yadda kakana ya yi noma. Ba zai yiwu ba a halin yanzu. Ya kamata a ƙawata shi, a zauna a kan tarakta a girbe masara da kuma kayayyakin da ake fitarwa,” in ji shugaban.

“Ina ganin hakan ya fi mana a Nijeriya. Kuma muna kan turbar aiwatar da wannan mataki. Ina da fiye da tarakta 2,000 da suke kan hanyar shigowa wannan ƙasa domin noman da ake da injuna,” a cewarsa.

Featured
Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Yawan Al’umma Na Iya Tsananta Matsalar Tsaro a Nijeriya-Bankin Duniya

October 20, 2025

Tsohon Gwamna Na Fuskantar Bincike Kan Zargin Hannu a Shirin Juyin Mulki

October 20, 2025

Kano: KIRS Ta Fitar Da Sabon Tsarin Biyan Haraji Ta Hanyar Fasahar Zamani

October 6, 2025

Takardar Sakandire Ta Isa Bayar Da Damar Rike Mukamin Siyasa — Shehu Sani

October 6, 2025

Kwalara ta kashe mutane 4,778 a Najeriya tsakanin shekarar 2020 zuwa 2024

October 6, 2025

NDLEA ta kama tarin ƙwayoyi da ake shirin safararsu zuwa Birtaniya

October 6, 2025
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Tsohon Gwamna Na Fuskantar Bincike Kan Zargin Hannu a Shirin Juyin Mulki

By WafsymOctober 20, 2025

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon gwamna daga wani yanki na kudu na ƙasar nan wanda…

Hawan Jini: Ƙungiyoyi Sun Yi Gargadi Kan Yaduwar Cutar a Nijeriya

September 27, 2025

Barkewar Cututtuka Uku Sun Tayar da Hankalin Hukumomin Lafiya a Nijeriya ‎

September 27, 2025

DALILAN DA YASA MUKAYI GWANJON TSAFFIN MOTOCIN DA MUKE GUDANAR DA AIKIN MU- NDLEA

April 13, 2025
© 2025 WDN HAUSA
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.