Gwamnatin jihar Sokoto, ta yi kira ga matan jihar su zama masu kula da mai da hankali yayin girki da tukwanen gas.
Gwamnan jihar Ahmad Aliyu ne ya bayyana haka lokacin zuyarar jaje bayan wata gobara ta tashi a yankin Igwai har ta yi sanadin mutuwar ɗaya daga cikin hadimansa.
Bayanai sun ce gobarar ta tashi ne sanadin girki da gas, lamarin da ya kai ga rasa ran da kuma asarar dukiya.
kula sosai a lokacin da suke amfani da gas domin girki a cikin gidajensu.
A lokuta da dama dai gas ɗin girki kan haddasa gobara a wasu sassan Najeriya, lamarin da a wasu lokutan kan zo da asarar rayuka.

