Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » NAPTIP Ta Ceto Mata Bakwai Ake Zargin Ana Shirin Safarar Su zuwa Ƙasar Iraki A Kano ‎
Afrika

NAPTIP Ta Ceto Mata Bakwai Ake Zargin Ana Shirin Safarar Su zuwa Ƙasar Iraki A Kano ‎

February 12, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
IMG 20260210 WA0031 768x576.jpg

Hukumar Hana Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP) ta ceto wasu mata bakwai  da ake zargin ana shirin safarar su zuwa ƙasar Iraki, bayan samamen da jami’anta suka kai wani otel a unguwar Sabon Gari da ke jihar Kano.

‎Hukumar ta bayyana cewa samamen ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da rundunar shiyyar Kano ta samu, lamarin da ya kai ga kuɓutar da matan masu shekaru tsakanin 21 zuwa 24.

‎Tirela Ta Murkushe Mutum Biyu Har Lahira A kaduna  ‎

‎Jami’in hulɗa da jama’a na NAPTIP a Kano, Mohammed Habib, ya ce jami’an hukumar sun kai farmakin ne a ranar Alhamis, inda suka kuma kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a safarar.

‎Ya ƙara da cewa binciken farko ya nuna an ɗauko matan ne daga kudancin Najeriya, inda aka yi amfani da Kano a matsayin wurin wucewa kafin a tura su zuwa Baghdad, babban birnin ƙasar Iraki, domin tilasta musu aiki.

‎A cewar hukumar, matan sun bayyana cewa wata mace da ake zargi a matsayin jagorar safarar ce ta shirya tafiyarsu, tare da haɗin gwiwar wani namiji da ya tsere, wanda jami’ai ke ci gaba da nema.

‎Tsarin tafiyar ya haɗa da sharadin cewa za su biya duk kuɗaɗen da aka kashe a kansu, tare da riba, bayan sun isa ƙasar da za su yi aiki.

‎Hukumar ta ce matan da aka ceto na hannunta a Kano, inda ake ba su kulawa, shawarwari da kuma taimakon farfaɗowa.

‎NAPTIP ta kuma bayyana cewa da zarar bincike ya kammala, za a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu.

‎Hukumar ta sake jaddada kudurinta na rushe hanyoyin safarar mutane tare da kira ga al’umma su kasance masu lura da kuma kai rahoton duk wani abu da ke nuna alamun safarar mutane.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

‘Ba zan ba ‘yan Najeriya kunya ba’ – Shugaba Tinubu

April 17, 2026

Wannan ce takarata ta ƙarshe – Atiku

April 15, 2026

Shekaru 12 bayan sace ƴan matan Chibok

April 15, 2026

Tsagin ADC ƙarƙashin David Mark ya kori Nafiu Bala da wasu bisa zargin yi wa jam’iyya zagon-ƙasa

April 15, 2026

Hukumomin yaƙi da cin hanci ba su taɓa gayyata ta ba — Pantami

April 14, 2026

An kama jami’an ƴansanda 6 tare da wasu mutane 3 bisa zargin ƙwace da satar mutane a Edo 

April 14, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

By WafsymApril 2, 2026

A Jihar Kano, ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda wasu masu anfani da…

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.