Fitaccen ɗan jarida kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Bash M Bash, ya ce durƙushewar harkokin masana’antu a Jihar Kano na daga cikin manyan dalilan da ke janyo koma baya a kasuwanci da tattalin arzikin jihar.
A cewarsa, raguwar ayyukan masana’antu ta raunana sana’o’i da kasuwanci, ta kuma rage guraben ayyukan yi da kudaden shiga ga al’umma. Ya ce idan har ana son Kano ta dawo da matsayinta na cibiyar kasuwanci a Arewacin Najeriya da ma ƙasar baki ɗaya, dole ne a dauki matakan farfaɗo da masana’antu.
Governor Yusuf Receives first female Northwest University VC, Prof. Amina Bayero
Bash M Bash ya yi kira ga manyan attajiran Kano, musamman Alhaji Aliko Dangote da Abdulsamad Rabiu na rukunin BUA, da su tashi tsaye wajen farfaɗo da tsofaffin masana’antu da ke yankunan Sharada, Challawa da Dakata, domin taimakawa wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar da samar da ayyukan yi ga matasa.
Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 18 ga Disamba, 2025, yayin wani taron yini biyu da ƙungiyar One Kano Agenda ta shirya, wanda aka gudanar a ɗakin taro na Jami’ar Khalifa Isyaka Rabiu (KHAIRUN), da ke Kofar Gadon Kaya a cikin birnin Kano.

