Gwamnan Jihar Sokoto, Dr. Ahmed Aliyu, ya gabatar da Kasafin Kudin Shekarar 2026 ga Majalisar Dokokin Jihar don yin duba da amincewa. Kasafin, mai taken ‘Kasafin Ci Gaban Tattalin Arziki da Al’umma,’ an tsara shi ne domin habaka ci gaban tattalin arziki da jin dadin jama’a a jihar.
Jimillar kasafin kudin naira ₦758.7 biliyan, inda bangaren tattalin arziki ya samu kaso mafi girma na 41%, bangaren zamantakewa kuma 37%. Bangaren tsaro an ware masa ₦45.26 biliyan domin karfafa zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.
Haɗin Kai ne Mabuɗin Dawo da Martabar Jihar Kano – Gwamnati
Bangaren lafiya an ware masa kaso 16%, wato ₦122.7 biliyan, ciki har da kammala gina Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Sokoto a Kasarawa, Asibitin Murtala Muhammad, da manyan asibitoci a Binji, Tambuwal, da Sokoto/Birni, tare da sayen motoci masu daukar marasa lafiya guda 21.
Bangaren ilimi an ware ₦115.9 biliyan domin inganta ingancin karatu da samar da kayayyakin more rayuwa ga makarantun firamare, sakandare da jami’o’i.
Bangaren aikin gona an ware ₦18.7 biliyan domin karfafa samar da abinci da tsaro na abinci ta hanyar tallafa wa manoma da taki, tractors, da sauran kayan aikin gona.
Bangaren ruwa an ware ₦41.1 biliyan, ciki har da shigar da wutar rana a hukumar ruwa da gyaran tsofaffin wuraren ruwa domin saukaka samun ruwan sha mai tsafta da inganta ban ruwa ga manoma.
Bangaren harkokin addini an ware ₦17.4 biliyan, ciki har da gyaran masallatan Sultan Bello da Sultan Abubakar III, da gina makarantun Islamiyya don karfafa ilimin addini.
Bangaren ayyuka da sufuri an ware ₦109.1 biliyan domin inganta hanyoyi da tsarin sufuri, ciki har da samar da motocin zamani masu jin dadin sufuri ga jama’a.
Gwamna Aliyu ya bayyana cewa kasafin an tsara shi ne da kaso 72% na manyan ayyuka da 28% na kashe-kashen yau da kullum, bisa shawarar IMF da Bankin Duniya, kuma duk ayyukan da aka kammala a shekarar da ta gabata an biya su ne daga kudaden tarayya da na cikin gida ba tare da aro ba.
Gwamnan ya ce kasafin yana nuna ra’ayin jama’a ne, bayan dogon tuntuba da masu ruwa da tsaki, kuma ya yi alkawarin aiki tukuru domin tabbatar da an aiwatar da shi yadda ya kamata.
Haka kuma, Gwamna ya gode wa Jagoran APC na Jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, kan shawarwari da goyon bayan da ya bayar, da kuma Majalisar Dokoki kan hadin kai a tsarin kasafin.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da aiki tare da gwamnati ta tarayya, karkashin shugabancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, domin ganin nasarar shirye-shirye da manufofin gwamnati.
Gwamna Aliyu ya tabbatar da jajircewar gwamnatin sa wajen ganin kasafin kudin ya kawo ci gaba da inganta rayuwar jama’a a jihar Sokoto.”

