Gwamnatin Jihar Kano ta gargadi malamai daga wajen jihar da kasa Baki daya da su daina yin magana ko sharhi da zai iya kawo cikas ga binciken da kwamitin shura ke gudanarwa kan zargin da ake yi wa Malam Lawan Abubakar Shu’aibu Triumph.
Rahotanni na Bayyana cewa, sakataren kwamitin, wanda kuma shi ne Kwamishinan Kasuwanci na jihar, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da ya gudanar a Kano.
Za’a yada zaman da zai gudana tsakanin majalisar Shura da Sheikh Lawan Triumph kai tsaye
Sagagi ya ce gwamnati ta lura da yadda wasu malamai daga wajen jihar ke tsoma baki a cikin batun kafin kammala binciken, yana mai cewa hakan na iya kawo tangarda ga kwamitin da ke gudanar da aikinsa cikin gaskiya da adalci.
Daga nan ya jaddada cewa kwamitin zai ci gaba da aikinsa ba tare da tsangwama ba, In da ya tabbatar da cewa sakamakon binciken zai fito bisa gaskiya da Adalci bayan kammala bincike.

