Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa za a yada zaman da za gudanar tsakanin majalisar Shura da Sheikh Lawan Triumph kai tsaye a kafafen yada labarai domin tabbatar da gaskiya da kuma kawar da shakku daga zukatan al’umma.
Jami’an Ƴan sanda Sun Kama Mai-Gadi Da Ake Zargi da Sace Yaro Ɗan Shekara Biyu
Sakataren majalisar Shura, Shehu Wada Sagagi, ne ya bayyana haka a taron manema labarai.
Ya ce za a fara da aikewa da malamin takardar gayyata wadda za ta ƙunshi rana da lokaci da za a sa shi ya bayyana a gaban kwamitin.

