An bayyana yadda talauci ke ingiza mutane sayar da ƙodarsu a Nijeriya, inda sama da ƙoda 651 aka sayar ba bisa ƙa’ida ba tsakanin 2015 zuwa 2020, tare da samun kimanin dala biliyan 41 a kasuwar fataucin gaɓoɓi ta ɓoye, a cewar Farfesa Aliyu Abdu na Jami’ar Bayero Kano.
Ya bayyana cewa wannan haramtacciyar sana’a ta zama wata ƙazamar kasuwanci ta duniya da ke haɗa dillalai marasa izini, likitoci da masu neman fita daga talauci ta hanyar sayar da sassan jikinsu.
Hukumar Alhazan Nijeriya ta fitar da farashin kujerar Aikin Hajjin 2026
Duk da cewa Dokar Kiwon Lafiyar Nijeriya ta 2014 ta haramta sayar da gaɓoɓi tare da hukunta masu laifi, raunin aiwatar da doka ya ba wa kasuwar bayan fage damar bunƙasa, inda ake yin tiyata a asirce kuma masu sayarwa ke fuskantar matsalolin lafiya da kuncin rayuwa.
Wannan matsalar ta kai ga manyan mutane kamar tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa Ike Ekweremadu kamuwa da laifin safarar ƙoda zuwa Burtaniya, yayin da wasu kwararru ke ganin cewa rashin adalci da talauci ne ginshiƙan wannan annoba.
Haka kuma, a shekarar 2021, wani asibiti a Abuja har sai da ya sanya alamar “Ba Mu Sayi Ƙoda!” bayan mutane da dama sun nemi siyar da sassan jikinsu saboda matsin tattalin arziki bayan annobar Korona.

