Allurar rigakafin ƙwayar cutar HIV da ake yi sau biyu a shekara, wadda masana suka yaba da ita a matsayin mafi inganci cikin shekaru da dama, ta jawo martani daga ƴan Najeriya bayan rahotanni da suka nuna za ta iya fitowa a kan kuɗi Naira dubu 70,000 ga kowanne mara lafiya a shekara.
Maganin, wanda ake kira lenacapavir, yanzu haka ana kasuwancinsa da sunan Yeztugo a Amurka ta hannun kamfanin Gilead Sciences a kan kuɗin da ya kai Dala 28,000 a shekara, kamar yadda jaridar Sunday PUNCH ta gano.
Gwamnan Kano Ya Mikawa Majalisa Sunayen Mutane Biyu Don Nada Su Kwamishinoni
Sai dai wata sabuwar yarjejeniya tsakanin manyan kamfanonin magunguna na Indiya, Hetero Labs Ltd. da Dr Reddy’s Laboratories, tare da abokan hulɗar duniya kamar Gates Foundation, Unitaid, Clinton Health Access Initiative da Wits RHI, na shirin samar da irin wannan maganin a farashi mai rahusa a ƙasashe masu ƙarancin albarkatu, ciki har da ƙasashen Afirka.
Saɓanin ƙwayoyin rigakafin PrEP da ake sha kullum, mutum na buƙatar allurar lenacapavir biyu ne kacal a shekara, inda kowace ɗaya ke kare mutum tsawon watanni shida. Masana sun bayyana wannan tsawon kariya a matsayin sauyi mai girma musamman ga mata da ke da matsala wajen shan magani kullum ko kuma waɗanda ke fuskantar ƙalubale wajen tattaunawa da abokan hulɗa kan amfani da kwaroron roba.
A kafafen sada zumunta kuwa, sanarwar sauƙin farashin maganin ta tayar da muhawara da jita-jita. Wasu sun yi iƙirarin cewa akwai boyayyun manufofi, wasu kuma suka danganta shi da shirin rage yawan jama’a da ƙasashen yamma ke goyon baya.
Wasu sun kafa hujja cewa ba dole ba ne a kawo irin wannan tsari alhali akwai hanyoyin da suka haɗa da jinkirta yin jima’i, amfani da kwaroron roba da kuma magungunan ARV. Sai dai wasu kaɗan sun yi maraba da wannan cigaba, suna mai nuna amfanin da zai iya kawowa wajen rage yaɗuwar cutar.

