Allah Ya yiwa tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari rasuwa a yau ranar Lahadi yana da shekara 82 da haihuwa.
Wata sanarwa da Garba Shehu mai magana da yawunsa ya fitar ta ce Buhari ya rasu a wani asibiti da ke birnin Landan.
Fadar shugaban Najeriya ta ce ya rasu da misalin ƙarfe 4:30 “sakamakon doguwar jinya”.
A wani labarin kuma, shugaba Ahmed Tinubu ya umarci Mataimakin sa Kashim Shettima da ya tafi Landan domin ya rako gawar Buhari zuwa gida Najeriya,, inda ake sa ran yi masa jana’iza a mahaifarsa watau garin Daura a jihar Katsina.
Allah Ya jikansa amin

