Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Jam’iyyun Adawa Sun Yi Fatali Da Sabuwar Dokar Zabe Ta 2026 Wacce Shugaba Tinubu Ya Amince Da Ita
Afrika

Jam’iyyun Adawa Sun Yi Fatali Da Sabuwar Dokar Zabe Ta 2026 Wacce Shugaba Tinubu Ya Amince Da Ita

February 27, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
IMG 20260227 WA0001

Wasu jam’iyyun siyasa na adawa a Nijeriya sun yi watsi da Dokar Zabe ta 2026 da Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da ita kuma Shugaba Bola Tinubu ya rattaba wa hannu, inda suka bukaci a fara sabon gyara cikin gaggawa kan abin da suka kira “tanade-tanade masu tauye dimokuradiyya” a cikin dokar.

A wani taron manema labarai mai taken “Kiran Gaggawa Don Ceto Dimokuradiyyar Nijeriya” da aka gudanar a Abuja a ranar Alhamis, shugabannin adawar sun ce dokar a yadda take yanzu na iya raunana gaskiya da sahihancin zabe tare da rage amincewar jama’a da tsarin kada kuri’a.

Yayin da yake karanta sanarwar taron, Shugaban Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Ahmed Ajuji, ya ce: “Muna bukatar Majalisar Dokoki ta Kasa ta fara sabon gyara ga Dokar Zabe ta 2026 nan take, domin cire dukkan tanade-tanade marasa kyau tare da tabbatar da cewa dokar ta yi daidai da muradi da burin ‘yan Nijeriya na samun sahihin zabe mai gaskiya, adalci da rikon amana a kasarmu. Kasa da haka ba zai wadatar ba.”

Daga cikin manyan jiga-jigan da suka halarci taron akwai tsohon Shugaban Majalisar Dattawa David Mark, tsohon gwamnan Jihar Osun Rauf Aregbesola, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, tsohon gwamnan Jihar Rivers Rotimi Amaechi, da kuma tsohon gwamnan Jihar Anambra Peter Obi, duk daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).

Manyan Labarai INEC ta sauya jadawalin Zaɓen 2027

Haka kuma, Shugaban NNPP na kasa Ahmed Ajuji da wasu fitattun ‘yan jam’iyyar ciki har da Buba Galadima sun halarta.

Tanade-tanade da Suka Jawo Ce-ce-ku-ce

Daya daga cikin muhimman batutuwan da suka fi daukar hankalin adawar shi ne gyaran Sashe na 60(3), wanda ya bai wa jami’an zabe damar komawa amfani da aika sakamakon zabe ta takarda idan aka samu matsalar sadarwa.

A cewar hadakar jam’iyyun, wannan tanadi na iya raunana wajabcin watsa sakamakon zabe ta na’ura, kuma zai iya samar da gibin da za a iya amfani da shi wajen magudi.

Sun ce kayayyakin fasahar zabe a Nijeriya sun isa su tallafa watsa sakamako ta na’ura a fadin kasa baki daya, suna mai nuni da bayanan da jami’an Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) suka tabɓ bayarwa a baya.

Jam’iyyun sun kuma yi watsi da gyaran Sashe na 84, wanda ya takaita hanyoyin zaben fidda gwani ga jam’iyyun siyasa zuwa zaben kai tsaye (direct primaries) ko kuma tsarin maslaha (consensus).

A cewarsu, wannan sauyi katsalandan ne cikin harkokin cikin gida na jam’iyyun siyasa, suna jaddada cewa zaben fidda gwani na wakilai (indirect primaries) hanya ce halastacciya a tsarin dimokuradiyya.

Sun kuma yi nuni da abin da suka kira kura-kurai a zabukan kananan hukumomi na Babban Birnin Tarayya (FCT) da aka gudanar kwanan nan, inda suka bayyana zaben a matsayin “cikakken magudi.” A cewarsu, hakan ya kara raunana amincewarsu da ikon tsarin zabe na samar da sahihin zabe a shekarar 2027.

Jam’iyyun sun ce matukar ba a sake duba Dokar Zabe ta 2026 baki daya ba, akwai barazanar ci gaba da raguwa amincewar jama’a da tsarin dimokuradiyyar Nijeriya.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda

April 25, 2026

Sarki Sunusi ya caccaki gwamnatin tarayya kan cigaba da ciyo bashi duk da janye tallafin mai

April 24, 2026

An tabbatar da naɗin Dr Muttaqha Darma a matsayin sabon ministan gidaje

April 24, 2026

El-Rufa’i ya sake zargin yunƙurin kama shi

April 21, 2026

Dole Najeriya ta samu tsaro – Babban hafsan tsaro

April 20, 2026

‘Ba zan ba ‘yan Najeriya kunya ba’ – Shugaba Tinubu

April 17, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda

By WafsymApril 25, 2026

Wani rahoton ‘yansanda ya bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na manyan laifuka…

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

April 2, 2026

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.