Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Jihohin Najeriya da suka fi yin kasafin kuɗi mai tsoka a 2026
Babban Labari

Jihohin Najeriya da suka fi yin kasafin kuɗi mai tsoka a 2026

February 20, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
970431c0 0b5b 11f1 b5e2 dd58fc65f0f6.png

Yayin da aka shiga wata na biyu a shekarar 2026, tuni gwamnonin jihohin Najeriya suka fara gudanar da wasu daga cikin ayyukan da suka tsara cikin kasafin kuɗin shekarar.

A wanann shekarar jihohin sun ƙara kuɗaɗe masu yawa cikin kasafinsu na shekarar da muke ciki, wani abu da ke nuna yadda jihohin ke samun ƙarin kuɗaɗe daga tarayya.

Shugaba Tinubu ya naɗa Sarkin Kano Aminu Ado Bayero a matsayin shugaban kwamitin ciyarwar Ramadan na Ƙasa

Jihohi da dama sun kafa hujja da burin gudanar da manyan ayyukan ci gaba wajen ƙara yawan kuɗaɗen da za su kashen a 2026.

Haka ma wasu jihohin sun ce ƙaruwar hauhwar farashin kayyaki da raguwar darajar kuɗin na daga cikin dalilan da suka kasafin kuɗaɗen nasu ya ƙaru.

A wannan shekarar jihohin ƙasar da dama ne suka yi kasafin da ya haura naira tiriliyan ɗaya, kamar yadda wasu bayanai da ƙungiyar BudgIT mai nazari kan kasafin kuɗi a ƙasar suka nuna.

Bisa dogaro da alƙaluman na BudgIT mun zaƙulo jihohin ƙasar 10 da suka yi kasafin kuɗi mai tsoka a 2026

Abia — ₦1.016 trillion

Jihar da ke yankin kudu maso gabashin Najeriya na daga cikin jihohin ƙasar 10 da suka yin kasafin kudi mai gwaɓi a wannan shekarar ta 2026.

Bayanai daga shafin BudgIT mai nazari kan kasafin kuɗaɗe a Najeriya sun nuna cewa jihar ta yi kasafin kuɗin da ya kai naira tiliyan 1.016.

A ranar 29 ga watan Disamban 2025 gwamnan jihar, Alex Otti, ya sanya hannu kan kasafin kuɗin jihar bayan amincewar majalisar dokokin jihar.

A cewar BudgIT, jihar ta ware naira biliyan 811.8 domin gudanar da manyan ayyuka, yayain da ta ware naira biliyan 204.4 domin gudanar da ayyukan yau da kullum.

A lokacin gabatar da kasafin gwamnan ya ce fannonin ilimi da gina tituna ne za su fi laƙume kuɗaɗe masu yawa.

Bisa ƙiyasin yawan jama’a na 2022, jihar na da yawan al’umma miliyan 4.143.

 

Niger — ₦1.31 trillion

Jihar Neja – wadda ke yankin Arewa ta Tskiyar Najeriya – ta shiga jerin jihohin ƙasar da suka yi kasafi mai gwaɓi a 2026.

Bayanai daga alƙaluman BudgIT na cewa jihar ta yi kasafin kuɗin da ya tasamma naira tiriliyan 1.310.

Jihar ta ware naira biliyan 761.6 domin gudanar da manyan ayyuka, yayin da ta ware naira biliyan 270.3 domin ayyukan yau da kullum.

Neja na da yawan al’umma miliyan 6.78 bisa ƙiyasin yawan jama’ar jihar na 2022.

A lokacin da yake gabatar kasafin kuɗin, gwamnan jihar Mohammed Umar Bago ya ce fannonin noma da ilimi da kuma lafiya ne za a fi bai wa fifiko.

Akwa Ibom — ₦1.390 trillion

Jihar Akwa Ibom da ke kudu maso kudancin Najeriya ta kasance cikin jihohin ƙasar masu gwaggwaɓan kasafi a 2026.

Alƙaluman BudgIT sun nuna cewa jihar ta gabatar da kasafin kudin naira tiriliyan 1.390.

Bayan da ƙungiyar ta fitar sun nuna cewa jihar ta ware wa fannin manyan ayyuka naira tiriliyan 1.035, yayin da fannin yau da kulluma ya samu naira biliyan 353.9.

A lokacin sanya hannu kan kasafi, gwamnan jihar, Umo Eno ya ce fannonin gina tituna da ilimi da lafiya za a fi bai wa fifiko.

Imo — ₦1.43 trillion

A cewar alƙaluman BudgIT, jihar ta yi kasafin naira tiriliyan 1.43 a wannan shekarar.

Alƙaluman sun nuna cewa fannin manyan ayyukan zai laƙume naira tiriliyan 1.201, yayain da ayyukan yau da kullum zai laƙume naira biliyan 238.5.

A lokacin sanya hannu kan kasafin kuɗin gwamnan jihar, Hope Uzodimma ya ce kasafin zai fi bayar da fifiko ga fannonin ayyukan more rayuwa da samar da ayyuka da kuma inganta rayuwar al’umma.

 

Kano — ₦1.47 trillion

Jihar Kano – da ke yankin arewa maso yammcin ƙasar – jiha ta biyu a arewacin ƙasar bayan Neja da kasafinsu ya haura naiya tiriliyan ɗaya.

Bayanai BudgIT sun nuna cewa jihar ta yi kasafin kuɗin da ya kai naira tiriliyan 1.47.

A ranar 31 ga watan Disamban 2025 gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan kasafin, bayan amincewar majalisar dokokin jihar.

Fannonin ilimi da abubuwan more rayuwa da lafiya ne kan gaba a kasafin.

Jihar Kano dai na da yawan al’umma kimanin miliyan 15.46, bisa ƙiyasin yawan jama’a na 2022.

 

Enugu — ₦1.62 trillion

Jihar Enugu ta kasance jiha ta uku cikin jihohin kudu maso gabashin ƙasar da suka yi kasafi mai gwaɓi a 2026.

Bayanai daga alƙaluman BudgIT sun nuna cewa jihar ta yi kasafi na naira tiriliyan 1.62.

Inda ta ware wa manyan ayyukan naira tiriliya 1.300, yayain da ayyukan yau da kullum ya samu naira biliyan 321.

Yayin gabatar da kasain gwamnan jihar, Peter Ndubuisi Mbah ya ce fannonin da kasafin zai fi bai wa fifiko sun haɗa da ilimi da lafiya da ayyukan more rayuwa da fannin sufuri.

Delta — ₦1.664 trillion

Jihar Delta mai arzikin man fetur da ke kudu maso kudancin Najeriya na kan gaba wajen yin kasafi mai gwaɓi a 2026.

Alƙaluman BudgIT mai sanya idanu kan harkokin kasafin kuɗi a Najeriya sun nuna cewa jihar ta yi kasafin naira tiriliyan 1.66 a wannan shekara.

A cewar BudgIT jihar ta ware naira tiriliyan 1.165 domin gudanar da manyan ayyuka, yayin da ta ware naira biliyan 499 ga fannin gudanarwar yau da kullum.

Yayin sanya hannu a kan kasafin, gwamnan jihar Sheriff Oborevwori ya ce kasafin ya bayar da fifiko ga fannonin samar da abubuwan more rayuwa da inmganta birane da tattalin arziki.

Ogun — ₦1.668 trillion

Jihar Ogun- wadda ke yankin kudu maso yammcin Najeriya – ce jiha ta takwas cikin jihohin ƙasar 10 da suka fi yin kasafi mai gwaɓi a 2026.

Jihar mai yawan manyan masana’antu a ƙasar ta yi kasafin da ya kai naira tiriliyan 1.66.

Yayin da ta ware wa manyan ayyuka naira tiriliyan 1.044, yayin da fannin gudanarwar yau da kullum ya samu naira biliyan 624.8.

Rivers — ₦1.854 trillion

Jihar Rivers ce jiha ta uku a yankin kudu maso kudancin Najeriya da kasafinta ya haura naira tiriliyan ɗaya.

Rivers – wadda ta fi kowace jiha ɗimbin arzikin man fetur a Najeriya – ta yi kasafin da ya kai naira tiriliyan 1.854.

Fannonin ayyukan more rayuwa da ilimi da lafiya ne manyan ɓangarorin da suka fi samun kuɗaɗe.

Lagos — ₦4.237 trillion

Jihar Legas ce ta fi kwoace jiha kasafi mai yawa cikin jihohin Najeriya a 2026.

Legas mai mayan tasoshin ruwa da masana’atu ta ware naira tiriliyan 4.337 a cewar alƙaluman BudgIT.

Jihar ta ware wa fannin manyan ayyukan naira tiriliyan 2.185, yayin fannin gudanarwar yau da kullum ya sam u naira tiriliyan 2.052.

Fannonin da suka fi samun fifiko sun haɗa da inganta rayuwar al’umma da gina abubuwan more rayuwa da kuma inganta tattalin arziki.

 

BBC HAUSA 

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Sojojin UAE biyu sun mutu a hatsarin jirgin sama – Ma’aikatar tsaro

March 10, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026

Mojtaba Khamenei Ya Gaji Mahaifinsa A Matsayin Jagoran Addinin Iran

March 9, 2026

Farashin litar man fetur ya zarce naira dubu 1 a sassan Najeriya

March 9, 2026

Mutanen da ake hasashen za su maye gurbin Mataimakin Gwamnan Kano

March 7, 2026

Yakin Amurka/Isra’ila da Iran: Lallai da ni za a zaɓi sabon shugaba a Iran – Trump

March 6, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Bincike Na Musamman

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

By WafsymMarch 9, 2026

‎Rundunar Kano Neighbourhood Watch Security Corps, wadda gwamnatin Jihar Kano ta kafa domin tallafawa hukumomin…

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026

KANO: Farashin Kayan Masarufi Ya Yi Tashin Gwauron Zabi Gabanin Shigowar Azumin Ramadan ‎ ‎

February 12, 2026

‎“Ya Kamata ‘Yan Jaridu Su Riƙa Nuna Tausayi, Hikima Da Mutunta Jinƙan Ɗan Adam wajen ɗauko labarai ‎ ‎ ‎—Comrade Abbas Ibrahim

January 21, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.