Fitacciyar ’yar gwagwarmayar kare haƙƙin ɗan Adam, Naja’atu Muhammad, ta zargi wasu ’yan siyasa, malaman addini da kuma sarakunan gargajiya a Arewacin Najeriya da cewa su ne suka gaza kare muradun yankin, lamarin da ta ce ya janyo koma-baya da tarin matsaloli a Arewa.
Naja’atu ta bayyana hakan ne a wata hira da ta yi da DCL Hausa, inda ta yi tsokaci kan makomar Arewacin Najeriya a siyasar 2027.
A cewarta, duk da yawan jama’a da albarkatun da yankin ke da su, rashin jagoranci nagari daga masu ruwa da tsaki ya hana Arewa cin gajiyar damar da ke gabanta.
Ta ce yawancin ’yan siyasa sun mayar da hankali ne kan ribar kansu da ta jam’iyyunsu, maimakon su fifita walwalar al’umma.
Haka kuma, ta ce wasu malaman addini sun shiga siyasa ta hanyar da ke haifar da rarrabuwar kai, yayin da wasu sarakunan gargajiya suka kasa tsayawa tsayin daka wajen kare muradun jama’arsu.
A cewarta, “Arewa na da dukkan damar ci gaba, amma abin takaici, shugabanni da masu tasiri sun fifita kansu, suka bar talakawa cikin talauci, rashin tsaro da koma-baya.”
Naja’atu Muhammad ta yi kira ga al’ummar Arewa, musamman matasa, da su waye su kuma nemi shugabanci na gaskiya da rikon amana a zaɓukan da ke tafe. Ta jaddada cewa idan ba a sauya salon siyasa ba kafin 2027, yankin na iya ci gaba da fuskantar ƙalubale masu tsanani.

