Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Ƙaɗan daga cikin jawabin farko na Shugaban Amurka Donald Trump
Afrika

Ƙaɗan daga cikin jawabin farko na Shugaban Amurka Donald Trump

January 21, 2025
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn

Jawabin farko na wa’adin mulkin Shugaba Donald Trump na biyu ya ƙunshi batutuwa kamar yadda yayi a jawabin wa’adinsa na farko: gama-garin suka ga ƙasar da ya karɓi ragamar mulkinta da kuma manyan alƙawurra na magance matsalolin.

Shekaru takwas da suka gabata, Donald Trump ya bayyana abin da ya kira “lalata Amurka ” kuma ya yi alƙawarin kawo ƙarshensa nan-take. A ranar Litinin, ya bayyana cewa “faɗuwar” ƙasar za ta zo ƙarshe nan-take, lamarin da zai kawo “lokacin da Amurka za ta fi kyau a tarihi.”

Matsalolin duniya

“Wata guguwar canji tana kaɗawa faɗin ƙasar. Haske na bazawa kan duniya gaba ɗaya, kuma Amurka za ta iya amfani da wannan damar fiye da yadda ta taɓa yi, amma daga farko dole mu kasance masu gaskiya game da ƙalubalen da muke fuskanta.”

Suka kan Biden

“A yanzu muna da wata gwamnatin da ba za ta iya warware ko ƙaramar matsala a cikin gida ba, yayin da kuma take ci gaba da shiga bala’o’i a ƙetare. Ta kasa kare ‘yan ƙasarmu masu bin doka da oda amma tana ba da mafaka da kariya ga masu laifi masu haɗari, waɗanda yawancin su daga kurkuku ko kuma asibitin taɓin hankali suke kuma suka shigo ƙasarmu ba bisa ƙa’aida ba daga ƙasashen duniya.”

Shiga ƙasar

“Zan ayyana dokar ta-ɓaci a bakin iyakar ƙasarmu na kudu. Nan take za’a dakatar da shiga ƙasar ta hanyar da ta saɓa wa doka, kuma za mu fara tsara yadda za mu mayar da miliyoyin baƙi masu laifi zuwa inda suka fito.”

“Za mu sake samun ‘yancin kanmu. Za mu sake tabbatar da tsaronmu. Za a sake daidaitar da ma’aunin adalci… za a sake mayar wa mutane imaninsu da arziƙinsu da dimokraɗiyyarsu da kuma ‘yancinsu… Daga yanzu faɗuwar Amurka ta ƙare.”

Zuwa duniyar Mars

“Za mu bi bayyanannen haƙƙinmu zuwa cikin taurari, inda za mu harba ‘yan sama-jannatin Amurka domin dasa tutar Amurka kan duniyar Mars.”

Yaƙe-yaƙen duniyar

“Muna da wata gwamnatin da ta ba da kasafin kuɗi mara iyaka wajen kare kan iyakokin ƙasashen ƙetare, amma ta ƙi kare kan iyakokin Amurka, ko kuma, mafi muhimmanci, kare mutanenta.”

Jinsi biyu kawai

“Zan kuma kawo ƙarshen tsarin gwamnati na ƙoƙarin shigar da launin fata da jinsi cikin duk wani fannin rayuwa, na gwamnati ne ko na mai zaman kansa… Daga yau, zai kasance a tsarin gwamnatin Amurka jinsi biyu ne kawai ake da shi, namiji da mace.”

“Muna da wani tsarin lafiya wanda ba ya iya biyan buƙata a lokacin bala’i, duk da haka ana ƙara kashe kuɗi a kansa fiye da ko ina a duniya. Kuma muna da wani tsarin ilimi da ke koya wa yaranmu su ji kunyar kawunansu, a yawan lokuta, su tsani ƙasarmu, duk da soyayyyar da muke matsananin nuna musu. Duk waɗannan za su sauya daga yau, kuma za su sauya cikin sauri.”

Tsarewar Allah

“Cikin shekaru takwas da suka gabata, an wahalar da ni tare da ƙalubalance ni fiye da ko wane shugaban ƙasa a tarihinmu na shekara 250… Waɗanda suka nemi su katse tafiyarmu sun yi ƙoƙarin ɗauke ‘yancina kuma ɗauke rayuwata. Kuma cikin ‘yan watannin da suka wuce, a cikin wani fili mai kyau a Pennsylvania, harshashin mai kisa ya bi ta kunne na, nan-take na ji kuma na yi imanin, kuma har yanzu, cewa an ceci rayuwata ne domin wani dalili. Allah ya cece ni ne domin in sake mayar da Amurka ƙasa mai girma”

Haƙo dai, haƙo dai

“Yawan kashe kuɗin gwamnati da ƙarin kuɗin makamashi ne suka janyo matsalar hauhawar farashi. Kuma shi ya sa a yau zan ayyana dokar ta-ɓaci kan makamashi . Za yi ta haƙo mai da iskar gas.”

Yaƙe-yaƙen haraji

“Nan-take zan fara sauya fasalin tsarin kasuwancinmu domin kare ma’aikata da kuma iyalan Amurka. Maimakon ƙaƙaba wa ‘yan ƙasarmu haraji domin azurta wasu ƙasashe, zamu sanya haraji kan ƙasashen ƙetare domin azurta ‘yan ƙasarmu.”

Featured
Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Yawan Al’umma Na Iya Tsananta Matsalar Tsaro a Nijeriya-Bankin Duniya

October 20, 2025

Tsohon Gwamna Na Fuskantar Bincike Kan Zargin Hannu a Shirin Juyin Mulki

October 20, 2025

Kano: KIRS Ta Fitar Da Sabon Tsarin Biyan Haraji Ta Hanyar Fasahar Zamani

October 6, 2025

Takardar Sakandire Ta Isa Bayar Da Damar Rike Mukamin Siyasa — Shehu Sani

October 6, 2025

Kwalara ta kashe mutane 4,778 a Najeriya tsakanin shekarar 2020 zuwa 2024

October 6, 2025

NDLEA ta kama tarin ƙwayoyi da ake shirin safararsu zuwa Birtaniya

October 6, 2025
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Tsohon Gwamna Na Fuskantar Bincike Kan Zargin Hannu a Shirin Juyin Mulki

By WafsymOctober 20, 2025

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon gwamna daga wani yanki na kudu na ƙasar nan wanda…

Hawan Jini: Ƙungiyoyi Sun Yi Gargadi Kan Yaduwar Cutar a Nijeriya

September 27, 2025

Barkewar Cututtuka Uku Sun Tayar da Hankalin Hukumomin Lafiya a Nijeriya ‎

September 27, 2025

DALILAN DA YASA MUKAYI GWANJON TSAFFIN MOTOCIN DA MUKE GUDANAR DA AIKIN MU- NDLEA

April 13, 2025
© 2025 WDN HAUSA
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.