Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Ambaliyar ruwa ta katse wasu manyan hanyoyin birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar
Afrika

Ambaliyar ruwa ta katse wasu manyan hanyoyin birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar

August 23, 2024
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
flood niger
flood niger

Wasu manyan hanyoyin fita da shiga na birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar mai kimanin mutum miliyan 1.5 sun kusan katsewa baƙi ɗaya, kana sama da mazauna birnin mutum 11,500 ne iftila’in ambaliyar ruwan sama ya shafa.

A watanni uku da suka wuce, ambaliyar ta yi sanadiyar mutuwar mutane 217 a faɗin ƙasar kana ta shafi sama da mutane 350,000, a cewar gwamnatin mulkin soji ta Nijar.

Da farko dai birnin Yamai ya tsira daga sauran yankunan kudu maso yammacin Nijar, amma a yanzu, kwale-kwale ne suka maye gurbin ƙanana da manyan motoci da babura wajen jigilar mutane da kayayyaki a kan hanyoyi.

Don samun damar isa zuwa ga sauran sassan ƙasar, ”dole sai mutum ya yi amfani da kwale-kwale tare da fatan samun abin hawa idan ya isa ɗaya bangaren,” in ji Habibulaye Abdoulaye, wani mazaunin wata unguwa da ke kewaye da ruwa.

Yawancin kamfanonin sufuri a Yamai sun dakatar da zirga-zirga zuwa sauran sassan Nijar.

Yayin da yake kallon yadda ambaliyar ruwan ke gudu ta gefen birnin, wani direban mota Ali Adamou ya shaida wa kamfanin dillacin labarai Faransa AFP cewa ruwan ya tafi da motarsa tare da wasu guda hudu.

“Na kusan mutuwa a lokacin da wata ƙaramar motar bas ta nutse,” in ji A damou

Gyaran hanyoyi

Masu tuƙa ƙananan jiragen ruwa suna karɓar CFA 500 kan duk jigilar da suka yi sai kuma ‘yan sanda da kwale-kwalen sojoji waɗanda suke taimakawa wajen jigilar mazauna da suka maƙale.

Daga gabashin babban birnin ƙasar, kamfanin gine-gine na ƙasar Faransa Sogea-Satom na ƙoƙarin sake buɗe hanyar ƙasa ta ɗaya, babbar hanyar da ta kai tsawon kilomita 1,500.

A gaɓar kogin Neja da ke birnin Yamai, masu aikin tono suna can suna aikin samar da hanyoyin wucewar ruwan, yayin da masu aikin sa kai da sojoji suke zagayawa don toshe wurare da ruwan ya yi wa illa da yashi.

A kwanakin baya ne aka sake buɗe hanya ɗaya tilo ta Tera da manyan motoci suke wucewa daga Yamai zuwa arewacin Burkina Faso.

“Hukumomin jihar suna yin dukkan mai yiwuwa don maido da zirga-zirgar ababen hawa,” in ji Ministan Sufuri, Kanar Salissou Mahaman Salissou.

Sai dai hukumomin Nijar na fargabar tsawaita zirga-zirgar na iya haifar da ƙaranci man fetur.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Yawan Al’umma Na Iya Tsananta Matsalar Tsaro a Nijeriya-Bankin Duniya

October 20, 2025

Tsohon Gwamna Na Fuskantar Bincike Kan Zargin Hannu a Shirin Juyin Mulki

October 20, 2025

Kano: KIRS Ta Fitar Da Sabon Tsarin Biyan Haraji Ta Hanyar Fasahar Zamani

October 6, 2025

Takardar Sakandire Ta Isa Bayar Da Damar Rike Mukamin Siyasa — Shehu Sani

October 6, 2025

Kwalara ta kashe mutane 4,778 a Najeriya tsakanin shekarar 2020 zuwa 2024

October 6, 2025

NDLEA ta kama tarin ƙwayoyi da ake shirin safararsu zuwa Birtaniya

October 6, 2025
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Tsohon Gwamna Na Fuskantar Bincike Kan Zargin Hannu a Shirin Juyin Mulki

By WafsymOctober 20, 2025

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon gwamna daga wani yanki na kudu na ƙasar nan wanda…

Hawan Jini: Ƙungiyoyi Sun Yi Gargadi Kan Yaduwar Cutar a Nijeriya

September 27, 2025

Barkewar Cututtuka Uku Sun Tayar da Hankalin Hukumomin Lafiya a Nijeriya ‎

September 27, 2025

DALILAN DA YASA MUKAYI GWANJON TSAFFIN MOTOCIN DA MUKE GUDANAR DA AIKIN MU- NDLEA

April 13, 2025
© 2025 WDN HAUSA
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.