Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Ƙungiyar ɗaliban makarantar FGC ta Kano sun kai ƙara gurin Tinubu bisa zargin yunƙurin wawashe filin makarantar
Afrika

Ƙungiyar ɗaliban makarantar FGC ta Kano sun kai ƙara gurin Tinubu bisa zargin yunƙurin wawashe filin makarantar

April 6, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
FB IMG 1775434603827

Kungiyar tsoffin daliban makarantar FGC ta Kano, mai suna FGCKOSA ta aike da ƙorafi ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu bisa abinda ta kira da wawashe katafaren filin makarantar.

Daily Nigerian Hausa ta gano cewa ma’aikatar ilimi ta ƙasa da haɗin gwiwar wani kamfani, Pluck Global Company Ltd. sun kulla yarjejeniyar yanka wa da yin gine-gine a filin, wanda a ke sa ran gobe Litinin za a ƙaddamar da aikin a harabar makarantar .

Shugaba Tinubu ya amince da biyan bashin ₦3.3tn don inganta wutar lantarki

Takardar korafin ta samu saka hannu na haɗin gwiwa da shugaban ƙungiyar na duniya, Shoyinka Shodunke da kuma wasu shahararrun mambobin ta da su ka haɗa da Sheikh Bashir Umar Aliyu, shugaban majalisar ƙoli ta shari’a ta kasa da Sheikh Rabiu Ishyaku Rabiu, shugaban rukunin kamfanin IRS.

Sauran da su ka rattaba hannu a takardar korafin sun haɗa da Engr. Suleiman Adamu, Galadiman Kazure, ⁠Alhaji Nasser Ahmed Dan Darman Lokoja da kuma ⁠Abdul Samaad Rabiu, shugaban rukunin kamfanonin BUA.

An kuma aike kwafin ta ga shugaban majalisar dattawa, shugaban majalisar wakilai da ministan ilimi da ƙaramin ministan ilimi da hukumomin ICRC, EFCC da ICPC, ƙungiyar ta ce sam ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa.

A cewar Shokunde, ƙungiyar ta samu labarin cewa ana kokarin handame filin wanda ya ƙunshi filayen wasanni da masallaci da sauran gine-gine masu muhimmanci a makarantar.

Ya kara da cewa ana shirin karbe filin makarantar ba tare da wata tuntuba ba, inda ya ce kamata ya yi ma a karawa FGC din girma na wai a rika rage ta na.

A cewar sa, FGCKOSA ta shafe sama da shekaru 30 tana kashe biliyoyin naira wajen cigaban makarantar ba tare da sa ran samun wata riba ta kuɗi ba.

“Har wata gidauniya muka bude mai suna FGCKOSA Foundation ba dan komai ba sai dan mu taimaka wajen cigaban FGC.

” A yanzu haka muna shirin sake tara biliyoyin naira domin mun cigaba da dorar da kokarin cigaban FGC, amma sai gashi mun samu wani mummunan labari.

“To ba za mu yarda da wannan ba. Za mu yi duk me yuwuwa mu dakile wannan yunkuri,” in ji Shokunde.

A karon gayyatar zuwa bikin ƙaddamar da aikin a filin da Daily Nigerian Hausa ta samu kwafi, Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ne babban bako a taron, sai kuma Kwamishinan Ƙasa, Abduljabbar Garko a matsayin babban mai jawabi sai kuma dattijon jam’iyyar APC na ƙasa, Mohammed Jamu Yusuf a matsayin mai jawabi ma biyu.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Hukumomin yaƙi da cin hanci ba su taɓa gayyata ta ba — Pantami

April 14, 2026

An kama jami’an ƴansanda 6 tare da wasu mutane 3 bisa zargin ƙwace da satar mutane a Edo 

April 14, 2026

Maki shida ne ya rage tsakanin Arsenal da Man City

April 13, 2026

Mutane sama da 50 sun rasu a kuskuren harin sojin sama a kasuwa

April 13, 2026

INEC ta ɗage aikin sabunta bayanan rajistar masu zaɓe a fadin ƙasa

April 11, 2026

Gwamnan Kano ya naɗa Bilkisu Maimota a matsayin shugabar ma’aikata ta jiha

April 11, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

By WafsymApril 2, 2026

A Jihar Kano, ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda wasu masu anfani da…

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.