Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Gwamnatin  Kano Ta Tura Dalibai 550  Domin Taimakawa Wajen Faɗaɗa Rajistar Katin Zaɓe A Fadin Jihar ‎
Afrika

Gwamnatin  Kano Ta Tura Dalibai 550  Domin Taimakawa Wajen Faɗaɗa Rajistar Katin Zaɓe A Fadin Jihar ‎

April 2, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
IMG 20260402 174619 925

Gwamnatin Jihar Kano ta tura dalibai 550 daga cibiyoyin ilimi tara domin taimakawa wajen faɗaɗa rajistar rajistar masu zaɓe CVR, a wani yunƙuri na ƙara ƙarfafa shiga harkokin dimokuraɗiyya a faɗin jihar.

‎Shugaban Kwamitin Ƙarfafa Rajistar Masu Zaɓe na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da shirin a filin wasanni  na Kofar Mata, inda ake gudanar da babban aikin rajistar masu zaɓe.

‎Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Abbas Ibrahim, Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai, ya fitar a madadin Kwamitin Ƙarfafa Rajistar Masu Zaɓe na Jihar Kano.

‎A cewar Waiya, an horas da daliban domin su taimaka wajen yin rajista ta yanar gizo (online pre-registration), domin rage cunkoso da kuma hanzarta aikin rajistar kai tsaye, musamman ga ɗalibai da sauran al’umma da ke fuskantar matsalar isa cibiyoyin rajista.

‎Ya ƙara da cewa daga cikin daliban, 100 sun fito ne daga Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi, yayin da sauran cibiyoyi takwas suka samar da dalibai 50 kowacce.

‎Waiya, wanda kuma shi ne Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, ya jaddada cewa rajistar masu zaɓe muhimmin hakki ne na ɗan ƙasa, wanda ke taka rawa wajen tabbatar da dimokuraɗiyya mai inganci.

‎Ya ce: “Wannan wata dama ce ga matasa su bayar da gudunmawa wajen gina dimokuraɗiyya. Jajircewarku da gaskiyarku za su taimaka wajen tabbatar da cewa an samu cikakken wakilci a tsarin shugabanci.”

‎Ya kuma buƙaci daliban da su gudanar da aikinsu da gaskiya da riƙon amana, tare da bin ƙa’idojin da aka shimfiɗa, yana mai gargadin su guji duk wani abu da zai kawo tarnaki ga sahihancin aikin.

‎A wani ɓangare kuma, ya bayyana cewa za a karrama daliban da suka fi ƙwazo da nuna nagarta wajen gudanar da aikinsu, domin ƙarfafa gasa mai kyau da kuma ɗaukar nauyi.

‎Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta taka muhimmiyar rawa wajen horas da daliban kan fannoni na fasaha da ɗabi’a da suka shafi rajistar masu zaɓe.

‎Haka kuma, shugabannin cibiyoyin ilimin da abin ya shafa sun halarci wajen ƙaddamar da shirin domin sanya ido, lamarin da ke nuna cikakken goyon bayan hukumomi ga shirin da kuma muhimmancin rawar da matasa ke takawa.

‎Wasu daga cikin daliban da aka zaɓa sun bayyana shirinsu na yin aiki tukuru domin tabbatar da nasarar shirin, tare da jaddada aniyarsu ta taimakawa wajen ƙara yawan masu rajista a jihar.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Gwamna Abba Ya Kaddamar da Kwamitin Yaƙi da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, Ya Sanya Hannu Kan Dokar Daba A Kano

July 22, 2026

“Rikicin Shaidar Zama Ɗan Ƙasa a Jos North Ya Ɗauki Sabon Salo, Sarakunan Gargajiya Sun Nemi Shiga Cikin Shari’a.”

July 11, 2026

Sarkin Gaya: Mallakar Katin Zaɓe Shi Ne Ginshiƙin Zaɓen Shugabanni Nagari

July 3, 2026

Sahihin ‎Labari Ke Tabbatar Da Amincewar Jama’a, Ba Gaggawar Wallafa Ba- Shugaban NUJ

July 1, 2026

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rushe Tsarin Karatu Mai Dauke Da JSS Da SS A Makarantun Sikandire A Najeriya

June 30, 2026

Jami’ar Northwest Kano Ta Kori Dalibai 34 Saboda Karya Dokokin Jarabawa ‎

June 30, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Ƙara Wa NDLEA Motoci Don Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ‎

June 29, 20267

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda

By WafsymApril 25, 2026

Wani rahoton ‘yansanda ya bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na manyan laifuka…

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

April 2, 2026

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.