Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Ayyuka Takwas Masu Tarin Lada A Kwanaki 10 Na Ƙarshen Watan Ramadan
Afrika

Ayyuka Takwas Masu Tarin Lada A Kwanaki 10 Na Ƙarshen Watan Ramadan

March 13, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
images 1 3

A yayin da aka shiga kwana goman ƙarshe a watan Ramadan, ga tunarwar wasu muhimman ayyukan lada da ya kamata a dage da su a cikin watan mai alfarma.

Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa riƙo da su yana da muhimmanci saboda tarin lada da aka tanadar wa mai aikata su:

Kotu ta haramta wa Aiyedatiwa neman wani wa’adin gwamna a Ondo

Itikafi: Ana so mutum idan mutum yana da hali ana ya shiga Itikafi, inda da lazimci bautar Allah. Mutum, namiji ko mace, na iya Itikafi na tsawon kwanakin ko na iya abin da ya sawwaka.

Neman daren Lailatul Kadar: Mutum ya dage wajen kirdado da neman dacewa da daren Lailatul Kadari, ta hanyar gabatar da salloli da addu’o’i da sauran ayyukan ibada, musamman a dararen mara a goman karshen watan Ramadan.

Sallah: Musamman Sallar Tarawihi da Tahajjud, baya ga yin sallolin farilla a cikin jam’i, da kuma yin nafilolin da ake yi kafin ko bayan sallolin na farilla.

Karatun Al-Kur’ani: A dage a yawaita karatun Al-Kur’ani domin a cikin watan Ramadan aka saukar da shi, a daren Lailatul Kadar, cikin kwana goman karshe.

Addu’o’i: A dage da addu’o’in neman garafa da rahamar Allah da aljannah da kuma dacewa da alherin duniya da lahira da kuma neman tsari daga wuta da kuma sharrin duniya da na lahira. Mutum na iya yin addu’a a lokutan da ake amsa addu’o’i kamar lokacin Sahur ko bude-bakin da lokacin da ake cikin azumin da cikin sujada ko a cikin sulusin karshe da dare da sauransu.

Umrah: Hadisi ya nuna wanda ya yi Umra a cikin goman karshe na Ramadan zai samu ladar yin aikin Hajji tare da Manzon Allah (SAW).

Zakka: Ana so duk Musulmi mai hali ya fitar da Zakkar Kono ya ba wa mabukata. Magidanci da da da hali zai fitar da sa’i daya (Mudun Nabi hudu) na hatsi, haka kuma zai fitar wa iyalansa da duk wanda yake ciyarwa. Ana iya fitarwa a bayar daga ranar 28 ga Ramadan har zuwa lokacin tafiya masallacin idi ranar Karamar Sallah.

Kabbarori: Ana yin kabbarori daga bayan faduwar ranar jajibirin Karamar Sallah, har zuwa lokacin da za a idar da sallar idin.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Hukumomin yaƙi da cin hanci ba su taɓa gayyata ta ba — Pantami

April 14, 2026

An kama jami’an ƴansanda 6 tare da wasu mutane 3 bisa zargin ƙwace da satar mutane a Edo 

April 14, 2026

Maki shida ne ya rage tsakanin Arsenal da Man City

April 13, 2026

Mutane sama da 50 sun rasu a kuskuren harin sojin sama a kasuwa

April 13, 2026

INEC ta ɗage aikin sabunta bayanan rajistar masu zaɓe a fadin ƙasa

April 11, 2026

Gwamnan Kano ya naɗa Bilkisu Maimota a matsayin shugabar ma’aikata ta jiha

April 11, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

By WafsymApril 2, 2026

A Jihar Kano, ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda wasu masu anfani da…

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.