Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Kotu Ta Ci Tarar Ƴansanda Naira Miliyan 30 Kan Ayyana Neman Sowore Ruwa A Jallo
Afrika

Kotu Ta Ci Tarar Ƴansanda Naira Miliyan 30 Kan Ayyana Neman Sowore Ruwa A Jallo

February 22, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
imaigpges 1 1 750x375

Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta yanke hukunci cewa Rundunar ‘Yansandan Nijeriya, ta aikata kuskure da ya saɓa ƙa’ida na ayyana ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin ɗan Adam kuma mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore, a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo a shekarar 2025.

Yayin yanke hukunci a ranar Juma’a, Mai shari’a Musa Kakaaki, ya bayyana cewa matakin da ’yansanda suka ɗauka ya saɓa wa tanade-tanaden kundin tsarin mulki tare da nuna amfani da iko da bai dace ba, inda ya jaddada cewa babu wanda ya zama mai laifi saboda amfani da ’yancin faɗar albarkacin bakinsa ko gudanar da zanga-zangar lumana ko kuma neman gwamnati ta ɗauki alhakin wani laifinta.

Abin da ya sa na shiga siyasa tsundum – Sheikh Pantami

Alƙalin ya ƙara da cewa ba za a ayyana mutum a matsayin wanda ake nema ba sai an samu sahihin sammacin kotu tare da ba shi cikakken sanarwa, kuma akwai hujjoji masu ƙarfi da ke nuna cewa yana guje wa shari’a da gangan.

Daga bisani kotun ta yanke hukuncin biyan diyyar Naira miliyan 30 a kan Rundunar ƴansanda da Sufeto Janar na ’Yansanda, Kayode Egbetokun, da Kwamishinan ’Yansandan Jihar Legas, Moshood Jimoh.

Idan ba a manta ba, a ranar 3 ga Nuwamban 2025, Kwamishinan ’Yansandan Jihar Legas, Moshood Jimoh, ya ayyana Omoyele Sowore a bainar jama’a a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo, inda ya zarge shi da yunƙurin shirya zanga-zangar a kan gadar jihar ta “Third Mainland Bridge“ sakamakon rushe wasu gine-gine a unguwar Oworonshoki.

 

 

LEADSHIP

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Rikicin ACF: Lokaci Ya Yi Na Rushe Tsohon Tsari Da Yin Garambawul —Abbas Ibrahim 

May 12, 2026

Za mu mayar da martani kan harin da aka kai wa jirgin ruwanmu – Koriya ta Kudu

May 11, 2026

Dalilin da ya sa na maida akwatin zaɓena Abuja – Pantami

May 11, 2026

Dangote na shirin gina matatar mai a ƙasar Kenya

May 11, 2026

Samar da Aminci, Shi Ne Farko — Dole a Kawar Da Siyasar Dauka Makamai Daga Fagen Siyasar Kano

May 5, 2026

Pantami ya yi watsi da tsarin maslaha bayan kin daukar shi a matsayin dan takarar gwamnan Gombe

May 3, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda

By WafsymApril 25, 2026

Wani rahoton ‘yansanda ya bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na manyan laifuka…

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

April 2, 2026

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.