Hukumar tsaron farin kaya a Najeriya ta shigar da tuhuma guda uku kan tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, bisa zargin shi da hannu bisa naɗar wayar mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro Malam Nuhu Ribadu.
A ƙarar da ta shigar mai lamba FHC/ABJ/CR/99/20262003 a safiyar yau Litinin a babbar kotun tarayya da ke babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, DSS ta tuhumi tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i da amincewa da aikata datsar wayar mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan tsaro.
Fiye da Kananan Yara Miliyan Biyu Ke Gararamba A Titunan Kano — NGO
Takaddar ƙarar ta zayyana cewa Malam Nasir El-Rufai a wani shiri da ya yi a kafar talabijin ta Arise ya tabbatar da aikata kutse tare da datsar wayar mai bai wa shugaban Najeriya kan tsaro Nuhu Ribadu, abin da ya saba da sashe na 12 (1) na dokar aikata laifuka ta Intanet da aka yi wa gyara a shekarar 2024.
Har wa yau a cikin takaddar ƙarar an zargi Malam Nasir El-Rufai da wasu mutane da yin amfani da wasu na’urori da suka datsi tattaunawar wayar tarho ta mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, laifin da ya saba da sashe na 131(2) na dokar sadarwa ta 2023.

