Ƙaruwar farashin sayen damar shiga shafukan Intanet, wato data, na ci gaba da jefa ɗaliban da ke dogaro da karatu daga nesa cikin mawuyacin hali, inda da dama ke korafin cewa hakan na kawo musu cikas wajen ci gaba da neman ilimi.
Wasu ɗaliban da wakilinmu ya zanta da su sun bayyana cewa tsadar data na hana su halartar darussan Intanet yadda ya kamata, tare da rage musu damar yin bincike, sauke littattafai da kuma shiga ajujuwan koyarwa ta yanar gizo.
Sanata Mas’ud El-Jibril Doguwa Ya Yi Allah-wadai Da Kashe Matar Aure Da ’Ya’yanta 6 A Kano
“Da farko ina iya sayen data in yi amfani da ita tsawon mako, amma yanzu ko cikin kwanaki biyu ba ta kai ba,” in ji wani ɗalibi daga Jihar kaduna. Ya ƙara da cewa wannan yanayi na tilasta masa zaɓi mai wahala tsakanin sayen data da biyan wasu muhimman buƙatun rayuwa.
Wannan matsala na zuwa ne a wani lokaci da al’ummar Najeriya ke fuskantar matsin tattalin arziƙi, sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da raguwar ƙarfin sayen kuɗi, lamarin da ya shafi yawancin iyalai da ɗalibai.
Masana harkar ilimi na gargaɗin cewa ci gaba da hauhawar farashin data na iya janyo koma baya a fannin ilimi, musamman ga matasa daga gidaje marasa ƙarfi, waɗanda ke amfani da Intanet wajen karatu, koyon sana’o’i da kuma samun ƙarin ilimi.
Suna kuma kira ga gwamnati da kamfanonin sadarwa da su samar da rangwame ko tsare-tsare na musamman domin tallafa wa ɗalibai, ta yadda tsadar data ba za ta zama shinge ga burinsu na samun ilimi ba.

