Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Yan siyasan Arewa da malaman addinin Arewa da sarakunan Arewa su ne suka sayar da Arewa ‎ ‎—Naja’atu Muhammad
Afrika

Yan siyasan Arewa da malaman addinin Arewa da sarakunan Arewa su ne suka sayar da Arewa ‎ ‎—Naja’atu Muhammad

December 31, 2025
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
Najatu Mohammed

Fitacciyar ’yar gwagwarmayar kare haƙƙin ɗan Adam, Naja’atu Muhammad, ta zargi wasu ’yan siyasa, malaman addini da kuma sarakunan gargajiya a Arewacin Najeriya da cewa su ne suka gaza kare muradun yankin, lamarin da ta ce ya janyo koma-baya da tarin matsaloli a Arewa.

‎Naja’atu ta bayyana hakan ne a wata hira da ta yi da DCL Hausa, inda ta yi tsokaci kan makomar Arewacin Najeriya a siyasar 2027.

‎Kotu ta tura Abubakar Malami da iyalansa gidan yarin Kuje

‎A cewarta, duk da yawan jama’a da albarkatun da yankin ke da su, rashin jagoranci nagari daga masu ruwa da tsaki ya hana Arewa cin gajiyar damar da ke gabanta.

‎Ta ce yawancin ’yan siyasa sun mayar da hankali ne kan ribar kansu da ta jam’iyyunsu, maimakon su fifita walwalar al’umma.

‎Haka kuma, ta ce wasu malaman addini sun shiga siyasa ta hanyar da ke haifar da rarrabuwar kai, yayin da wasu sarakunan gargajiya suka kasa tsayawa tsayin daka wajen kare muradun jama’arsu.

‎A cewarta, “Arewa na da dukkan damar ci gaba, amma abin takaici, shugabanni da masu tasiri sun fifita kansu, suka bar talakawa cikin talauci, rashin tsaro da koma-baya.”

‎Naja’atu Muhammad ta yi kira ga al’ummar Arewa, musamman matasa, da su waye su kuma nemi shugabanci na gaskiya da rikon amana a zaɓukan da ke tafe. Ta jaddada cewa idan ba a sauya salon siyasa ba kafin 2027, yankin na iya ci gaba da fuskantar ƙalubale masu tsanani.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Yadda dawowar sanyi ya sauya al’amura a Kano

January 12, 2026

Majalisar Dokokin Legas Ta Amince Da Kasafin Kuɗin 2026 Na Naira Tiriliyan 4.4

January 9, 2026

Sheikh gumi ya soki farmakin saman Amurka a Najeriya

December 26, 2025

Jinkirin aiwatar da dokokin haraji zai cutar da ma’aikata da talakawa — shugaban kwamitin fadar shugaban ƙasa 

December 22, 2025

An Kama ‘Yan Mata Biyu da Laifin Yunkurin Shigar da Miyagun Kwayoyi Cikin Gidan Yari a Kano

December 22, 2025

Gwamnatin Tarayya Ta Bayar Da Hutun Kirsimeti Da Sabuwar Shekara

December 22, 2025
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Tsohon Gwamna Na Fuskantar Bincike Kan Zargin Hannu a Shirin Juyin Mulki

By WafsymOctober 20, 2025

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon gwamna daga wani yanki na kudu na ƙasar nan wanda…

Hawan Jini: Ƙungiyoyi Sun Yi Gargadi Kan Yaduwar Cutar a Nijeriya

September 27, 2025

Barkewar Cututtuka Uku Sun Tayar da Hankalin Hukumomin Lafiya a Nijeriya ‎

September 27, 2025

DALILAN DA YASA MUKAYI GWANJON TSAFFIN MOTOCIN DA MUKE GUDANAR DA AIKIN MU- NDLEA

April 13, 2025
© 2026 WDN HAUSA
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.