Shugaban Kwamitin fadar shugaban kasa kan Sauye-sauyen Haraji, Taiwo Oyedele, ya gargaɗi cewa jinkirta aiwatar da sabbin dokokin haraji bayan 1 ga Janairu, 2026, zai ƙara nauyin haraji ga ma’aikata da ’yan kasuwa a Najeriya.
Oyedele ya ce kashi 98 cikin 100 na ma’aikata za su ci gaba da fuskantar haraji iri-iri, yayin da ’yan kasuwa za su rasa rangwamen da sabbin dokokin suka tanada.
Ya bayyana haka ne a shirin The Morning Brief na gidan talabijin na Channels .
An Kama ‘Yan Mata Biyu da Laifin Yunkurin Shigar da Miyagun Kwayoyi Cikin Gidan Yari a Kano
Gargaɗin nasa na zuwa ne a lokacin da ake ta ce-ce-ku-ce kan zargin cewa dokokin da aka fitar a gazette ba su yi daidai da waɗanda majalisar tarayya ta amince da su ba.
Wasu ’yan siyasa da ƙungiyoyin fararen hula sun yi kira da a dakatar da aiwatar da dokokin.
Sai dai Oyedele ya ce maimakon dakatarwa, ya kamata a aiwatar da dokokin kamar yadda majalisar tarayya ta amince da su, tare da gyara duk wani kuskure da aka gano daga baya.
Dokokin sauye-sauyen haraji guda huɗu da shugaba Bola Tinubu ya rattaba wa hannu ana sa ran za su fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026, domin sauƙaƙa tsarin biyan haraji, faɗaɗa tushen haraji da inganta tara kuɗaɗen shiga a ƙasar.

