Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na aiwatar da kudirin One Kano agenda, yana mai cewa haɗin kai da aiki tare a matsayin al’umma ɗaya su ne mabuɗin dawo da martabar jihar da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa.
Gwamnan, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Umar Farouk Ibrahim, ya wakilta, ya ce gwamnatin jihar za ta ba wa shirin cikakken goyon baya, yana mai jaddada cewa lokaci ya yi da al’ummar Kano za su ajiye banbance-banbance su haɗa kai domin ceto jihar.
DRDI organizes One-Day Training to Raise Public Awareness on Local Government Budgeting
Ya ce shekaru kusan 40 zuwa 50 da suka gabata Kano na daga cikin jihohin da ake koyi da su a fannoni da dama, ciki har da ilimi, kasuwanci, noma, ci gaban matasa, al’adu da kuma ƙarfafa sarakunan gargajiya da ake girmamawa a faɗin ƙasar.
A cewarsa, dawo da wannan matsayi na buƙatar haɗin kai tsakanin ‘yan siyasa, al’umma da masu ruwa da tsaki daga kowane ɓangare. Ya ƙara da cewa hakan zai taimaka wajen fuskantar manyan ƙalubale kamar shan miyagun ƙwayoyi, tare da samar da zaman lafiya da bunƙasar tattalin arziki a jihar.
Sakataren Gwamnatin ya bayyana cewa gwamnatin NNPP ta cika kusan kashi 85 cikin 100 na alkawurran da ta yi wa al’umma a lokacin yaƙin neman zaɓe, yana mai tabbatar da cewa ana kan kammala sauran kashi 15 cikin 100. Ya kuma bayyana cewa gabanin zaɓukan fidda gwani na shekarar 2026, gwamnatin na shirin sake sabunta alkawurran ci gabanta domin tabbatar da Kano mai wadata.
A nasa jawabin, Kwamishinan Yaɗa Labarai, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya yi kira ga jama’a da su rungumi sadaukarwa da jajircewa a aikin sake gina Kano. Ya ce gwamnatin na tallafa wa tsofaffi da ‘yan fansho da suka shafe shekaru suna hidimtawa jihar, tare da bayyana shirin faɗaɗa irin wannan tallafi zuwa ga tsofaffin shugabannin kananan hukumomi da kansiloli da suka yi aiki tsakanin 2014 zuwa 2023.
Taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki ya samu halartar ƙungiyoyin matasa, ƙungiyoyin farar hula da sauran jama’a, inda aka tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban Kano da hanyoyin magance matsalolin zamantakewa da tattalin arziki na jihar, a salo na neman mafita mai amfani.

