Kungiyoyi masu zaman kansu da ma’aikatan kiwon lafiya sun bayyana damuwarsu kan yadda cutar hawan jini ke yaduwa a Nijeriya, inda suka ce akwai buƙatar ɗaukar matakan gaggawa domin rage haɗarin da cutar ke haifarwa.
Shugaban wata ƙungiya mai lura da lafiyar jama’a ya bayyana cewa ɗaya daga cikin muhimman ayyukan da suka gudanar shi ne samar da takardar bayanai kan cututtukan da ke kama zuciya wacce gwamnati za ta iya amfani da ita wajen tsara manufofi.
Ƙungiyar ta haɗa kai da Gwamnatin Tarayya wajen horar da ma’aikatan jinya kan yadda za su kula da masu fama da hawan jini a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko, musamman a lokutan da babu ƙwararren likita.
Hawan jini na daga cikin cututtukan da ba a yada su (Non-Communicable Diseases – NCDs), kuma na haddasa matsaloli masu tsanani kamar bugawar zuciya, shanyewar jiki, ciwon ƙoda da ma kisa. Bincike ya nuna cewa kashi 30% zuwa 40% na mutane a Nijeriya na fama da cutar, inda mafi yawan su ba su sani ba.
Masana sun yi gargadin cewa Nijeriya na fuskantar annobar hawan jini ta shuru, saboda cutar ba ta bayyana alamarta har sai lokacin da matsala mai tsanani ta taso. Abin takaici, da yawa daga cikin masu fama da cutar ba sa samun kulawa yadda ya kamata. Ƙarin matsalolin sun haɗa da yawan cin gishiri, rashin motsa jiki, shan taba, shan barasa, ƙarancin asibitoci da tsadar magunguna. Masana na ƙarfafa mutane da su dauki matakan kariya tun daga yau domin rage haɗarin kamuwa da ciwon.

