Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Zan ƙara buɗe wa ‘yan Nijeriya da kamfanoni hanyoyin samun bashi ga yan kasa – Tinubu
Afrika

Zan ƙara buɗe wa ‘yan Nijeriya da kamfanoni hanyoyin samun bashi ga yan kasa – Tinubu

January 1, 2025
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu, ya ce gwamnatinsa za ta ƙara buɗe hanyoyin samun bashi ga ‘yan ƙasar tare da masana’antu domin ƙarfafa tattalin arziƙin ƙasar a cikin sabuwar shekarar 2025.

A jawabinsa ga ‘yan ƙasar wanda ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta yi wannan ne ta hanyar kafa wani kamfani da zai kasance asusun tabbatar da biyan bashi na ƙasa wato National Credit Gurantee Company domin rage hatsarin ba da bashi ga bankuna da kamfanoni.

“Kamfanin da ake sa ran zai fara aiki kafin tsakiyar shekara zai kasance na haɗin-gwiwa ne tsakanin ma’aikatun gwamnati kamar bankin masana’antu da hukumar ba da bashi ga mutane (Nigerian Consumer Credit Corporation) da kamfanin zuba jari na Nijeriya da ma’aikatar kuɗi ta Nijeriya da ‘yan kasuwa da kuma hukumomin ƙasa da-ƙasa,” in ji shugaban.

“Wannan matakin zai ƙarfafa aminci a tsarin kuɗin ƙasar tare da ƙara hanyar samun bashi da kuma tallafa wa waɗanda ba su cika samun dama ba irin su mata da matasa. Zai kawo ci-gaba da farfaɗo da masana’antu da kuma inganta rayuwar al’umarmu,” a cewar Tinubu.

Haka kuma shugaban ya ce gwamnati za ta yi ƙoƙarin tabbatar da cewa hauhawar farashi ta ragu daga kashi 34.6 cikin 100 zuwa kashi 15 a cikin 100 a shekarar 2025 ta hanyar haɓaka harkar noma tare da inganta haɗa muhimman magunguna a cikin gida.

Shugaban, da ya nemi ‘yan ƙasar su goya masa baya wajen tabbatar da cewa tattalin arziƙin ƙasar ya kai na dala tiriliyon ɗaya, ya ce dole ‘yan ƙasar su inganta biyayyarsu ga ƙasar domin ta iya cim ma muradunta.

“Gaskiyar ‘yan ƙasa da kuma amincewarsu da ƙasar na da muhimmanci wajen nasarar Muradun Sabon Fata,” in ji shugaban wanda ya ce gwamnati za ta mayar da hankali wajen wayar da kan jama’a game da halayen da suka kamata ‘yan ƙasar su kasance suna da su.

Featured
Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Za mu mayar da martani kan harin da aka kai wa jirgin ruwanmu – Koriya ta Kudu

May 11, 2026

Dalilin da ya sa na maida akwatin zaɓena Abuja – Pantami

May 11, 2026

Dangote na shirin gina matatar mai a ƙasar Kenya

May 11, 2026

Samar da Aminci, Shi Ne Farko — Dole a Kawar Da Siyasar Dauka Makamai Daga Fagen Siyasar Kano

May 5, 2026

Pantami ya yi watsi da tsarin maslaha bayan kin daukar shi a matsayin dan takarar gwamnan Gombe

May 3, 2026

Kwankwaso da Obi sun koma jam’iyyar NDC

May 3, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda

By WafsymApril 25, 2026

Wani rahoton ‘yansanda ya bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na manyan laifuka…

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

April 2, 2026

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.