Barcelona ta kara yin rashin nasara karo na biyu a ɗaukaka kakar yi wa ɗan wasan tawagar Sifaniya, Dani Olmo rijista kafin 1 ga watan Janairun 2025.
Cikin watan Agusta, Barcelona ta sayi ɗan ƙwallon daga RB Leipzig mai buga Bundesliga kan £51m.
To sai dai Barcelona ta yi masa rijista zuwa rabin kakar bana, saboda kar ta karya dokar kashe kudi daidai samu ta hukumar La Liga.
Wata kotu ce ta hana Barcelona kara yi wa Olmo rijista a makon jiya, sannan a karo na biyu ta jaddada hukunci ranar Litinin.
Hakan na nufin Olmo ba zai sake buga wa Barcelona tamaula ba daga ranar 1 ga watan Janairun 2025.
A cewar La Liga, kotun ta yi watsi da kokarin yi wa Olmo rajistar saboda “babu daya daga cikin sharuddan da suka wajaba na ka’ida da aka cika”.
Mahukuntan sun kara da cewar kwamitin tabbatar da kasafin kudin ta ne ya dauki matakin kin yi wa Olmo rijistar, wanda matashi ne a Barcelona amma ya tafi Dinamo Zagreb mai shekaru 16.
Yanzu an bar Barcelona da tunanin yadda za ta mallaki Olmo, idan ba haka ba zai kasance bai da ƙungiya daga Janairu, wanda aka ce ƙungiyoyin Premier League da yawa na zawarcinsa.
Wasu rahotanni daga Sifaniya na cewa Barcelona na shirin sayar da wajen zaman manyan baƙi a Camp Nou, wanda zai kai Yuro miliyan 100, amma sai mahukuntan La Liga sun amince.
Olmo, wanda ya taka rawar gani da ta kai Sifaniya ta lashe Euro 2024 a Jamus, ya ci wa Barcelona ƙwallo shida a karawa 15 a kakar nan.
Barcelona tana ta ukun teburin La Liga da tazarar maki uku tsakani da mai jan ragama Atletico Madrid.