Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da nasarar gwamnonin jihohin Kogi da Bayelsa da kuma jihar Imo dake kudancin kasar.
A hukuncin da ta yanke ranar Juma’a Kotun ta tabbatar da Sanata Duoye Diri na jam’iyyar PDP, a matsayin halastaccen zaɓaɓɓen gwamnan jihar Bayelsa, bayan da ta yi watsi da ƙarar da Timipre Silva na jam’iyyar APC, ya shigar gabanta don ƙalubalantar nasarar da Mista Diri ya samu a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar 11 ga watan Nuwamban 2023.
Haka kuma kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Usman Ododo na APC a matsayin gwamnan jihar Kogi, bayan watsi da ƙorafin Murtala Ajaka na na SDP
Kotun ta ce ta tabbatar da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke ranar 27 ga watan Mayun da ya gabata, wadda ta tabbatar da Ododo.
A dai ranar Juma’ar ne kuma kotun ƙolin ta tabbatar da nasarar gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma a zaɓen na ranar 11 ga watan Nuwamba.
Kotun ta tabbatar da nasarar Uzodinma ne bayan fatali da ƙorafin ɗan takarar jam’iyarra PDP, Samuel Anyanwu, saboda rashin gamsassun hujjoji agaban kotun.