Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Tirela Ta Murkushe Mutum Biyu Har Lahira A kaduna  ‎
Babban Labari

Tirela Ta Murkushe Mutum Biyu Har Lahira A kaduna  ‎

February 12, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
Tirela

‎Wata tirela ta murkushe mutum biyu har lahira a kan babban titin Nnamdi Azikiwe da ke cikin garin Kaduna a daren Talata.

‎Shaidun gani da ido sun ce mutanen da abin ya rutsa da su, namiji da mace, suna kan babur ne lokacin da tirelar ta kwace ta taka su, inda suka mutu nan take wajen misalin karfe 9:00 na dare.

‎Shugaba Tinubu Ya Naɗa Ambasada Ismail Abba Yusuf A Matsayin Shugaban NAHCON

‎Wani shaidan da ya zanta da Wakila Jaridar AMINIYA ya ce lamarin ya tayar masa da hankali, inda ya ce, “Gaskiya abin babu dadi. Namijin da macen suna kan babur, kuma babu wanda ya san daga inda suka fito. Nan take duka su biyu suka mutu.”

‎Daga bisani jami’an ’yan sanda sun isa wurin tare da dauke gawarwakin zuwa asibiti.

‎Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) na shiyyar Kaduna, Tijjani Iliyasu, ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin.

‎Ya ce sun samu rahoton wata tirela ta taka mutum biyu a kan hanyar, inda ya kara da cewa ana aikin gyaran hanya a wurin, wanda hakan ke bukatar direbobi su yi hakuri tare da tuki cikin natsuwa da kulawa.

‎“Ana aikin gyaran hanyar, don haka ya zama dole direbobi su yi hakuri su kuma guji tukin ganganci. Abin takaici, da yawa daga cikinsu ba sa hakuri, kuma wannan ce matsalar,” in ji shi.

‎Ya kuma yi kira ga masu ababen hawa da su rika bin dokokin hanya tare da yin tuki cikin hakuri da natsuwa domin rage yawaitar haduran da ake samu a hanyoyin kasar nan.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Rikicin ACF: Lokaci Ya Yi Na Rushe Tsohon Tsari Da Yin Garambawul —Abbas Ibrahim 

May 12, 2026

Za mu mayar da martani kan harin da aka kai wa jirgin ruwanmu – Koriya ta Kudu

May 11, 2026

Dalilin da ya sa na maida akwatin zaɓena Abuja – Pantami

May 11, 2026

Dangote na shirin gina matatar mai a ƙasar Kenya

May 11, 2026

Samar da Aminci, Shi Ne Farko — Dole a Kawar Da Siyasar Dauka Makamai Daga Fagen Siyasar Kano

May 5, 2026

Pantami ya yi watsi da tsarin maslaha bayan kin daukar shi a matsayin dan takarar gwamnan Gombe

May 3, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda

By WafsymApril 25, 2026

Wani rahoton ‘yansanda ya bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na manyan laifuka…

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

April 2, 2026

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.