Gwamnonin yankin Arewa tare da sarakunan gargajiya sun ba da shawarar a dakatar da dukkan ayyukan hakar ma’adinai a Arewa na tsawon watanni shida, sakamakon tsananin damuwa kan tabarbarewar tsaro a yankin.
An bayyana wannan shawarar ne a cikin sanarwar bayan taron haɗin gwiwa na Gwamnonin Jihohin Arewa da Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa, wanda aka gudanar a fadar gwamnatin Sir Kashim Ibrahim da ke Kaduna.
A cewar sanarwar, dakatar da ayyukan hakar ma’adinai zai ba da damar tantance alakar da ke tsakanin hakar ma’adinai, matsalolin tsaro, da ta’addanci a yankin, tare da samar da lokacin da hukumomi za su sake tsara matakan kare rayuka da dukiyoyi.

