Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Nijeriya za ta dogara da sayen jiragen yaƙi daga Turkiyya domin kawo ƙarshen ta’addanci – Muhammad Badaru
Afrika

Nijeriya za ta dogara da sayen jiragen yaƙi daga Turkiyya domin kawo ƙarshen ta’addanci – Muhammad Badaru

November 21, 2024
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
bad
bad

Ministan Tsaron Nijeriya Mohammed Badaru Abubakar ya ce karshen ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a Najeriya ya kusa, adaidai lokacin da kasar ke samun karin kayan aikin soja daga Turkiyya.

Minista Badaru ya yi wannan jawabin ne a sansanin sojin saman Nijeriya da ke jihar Katsina a arewacin kasar, yayin kaddamar da jiragen yaki masu saukar ungulu na T129 ATAK guda biyu, wadanda kasar ta saya daga kasar Turkiyya.

“Karshen ayyukan ‘yan ta’adda da ‘yan daba masu dauke da makamai a kasar ya kusa,” in ji Ministan Tsaron Nijeriya a wajen taron a farkon makon nan.

Ya kuma yi kira ga rundunar sojin sama da ta hada kai da sojojin kasa da sauran masu ruwa da tsaki domin samun nasara a kan makiya kasar.

Mista Abubakar ya bukaci jami’an tsaro da su ƙara zage damtse wajen ganin sun kawar da ‘yan ta’adda masu dauke da makamai, da kuma kungiyoyin ta’addanci na Boko Haram da ISWAP, yana mai jaddada cewa suna barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da walwala.

Nijeriya ta ƙulla yarjejeniya da kamfanin ƙera jiragen yaƙi na Turkiyya, TAI, na sayen jirage masu saukar ungulu na T-129 ATAK guda shida domin bunkasa karfin sojojinta na sama.

Kasar ta Afirka ta Yamma ta samu biyu daga cikin jirage masu saukar ungulu na yaki a watan Fabrairu, biyu kuma a watan Satumba, yayin da ake kan aikin ƙera sauran biyun.

A cikin ‘yan shekarun nan, kasashen biyu sun samu ci gaba sosai, kuma ana sa ran za su rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniyar tsaro ta sama da dala biliyan biyu nan gaba, a cewar majiyoyin.

Jami’an Nijeriya karkashin jagorancin Ministan Tsaro sun ziyarci Turkiyya a watan Fabrairun wannan shekara inda suka tattauna da sakataren masana’antun tsaro na fadar shugaban kasar ta Jamhuriyar Turkiyya Farfesa Dr Haluk Görgün.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Yawan Al’umma Na Iya Tsananta Matsalar Tsaro a Nijeriya-Bankin Duniya

October 20, 2025

Tsohon Gwamna Na Fuskantar Bincike Kan Zargin Hannu a Shirin Juyin Mulki

October 20, 2025

Kano: KIRS Ta Fitar Da Sabon Tsarin Biyan Haraji Ta Hanyar Fasahar Zamani

October 6, 2025

Takardar Sakandire Ta Isa Bayar Da Damar Rike Mukamin Siyasa — Shehu Sani

October 6, 2025

Kwalara ta kashe mutane 4,778 a Najeriya tsakanin shekarar 2020 zuwa 2024

October 6, 2025

NDLEA ta kama tarin ƙwayoyi da ake shirin safararsu zuwa Birtaniya

October 6, 2025
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Tsohon Gwamna Na Fuskantar Bincike Kan Zargin Hannu a Shirin Juyin Mulki

By WafsymOctober 20, 2025

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon gwamna daga wani yanki na kudu na ƙasar nan wanda…

Hawan Jini: Ƙungiyoyi Sun Yi Gargadi Kan Yaduwar Cutar a Nijeriya

September 27, 2025

Barkewar Cututtuka Uku Sun Tayar da Hankalin Hukumomin Lafiya a Nijeriya ‎

September 27, 2025

DALILAN DA YASA MUKAYI GWANJON TSAFFIN MOTOCIN DA MUKE GUDANAR DA AIKIN MU- NDLEA

April 13, 2025
© 2025 WDN HAUSA
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.