Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da Kwamitin Haɗin Gwiwa na Hukumomi kan Yaƙi da Shan Miyagun Ƙwayoyi, tare da sanya hannu kan Dokar Zartarwa da za ta ƙarfafa yaƙi da daba da sauran ayyukan ta’addanci a faɗin jihar.
Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
Sakamakon Binciken Jami’ar Northwest Kano Ya Haskaka Matsalolin Lafiyar Al’umma a Tofa
Gwamna Abba ya ce shan miyagun ƙwayoyi na daga cikin manyan matsalolin da ke addabar matasan Kano, yana mai cewa matsalar tana haddasa aikata laifuka, rusa zaman lafiyar iyalai, raunana tattalin arziki da kuma kawo cikas ga zaman lafiya a cikin al’umma.
Ya bayyana cewa sabon kwamitin zai haɗa kai da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki wajen tattara bayanan sirri, aiwatar da doka, wayar da kan jama’a, da kuma kula da masu fama da shaye-shaye domin rage yaɗuwar matsalar.
Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta samar wa kwamitin isassun kuɗaɗe, motocin aiki, ofisoshi, kayan aiki da kuma kariyar jami’an tsaro domin sauƙaƙa masa gudanar da ayyukansa cikin inganci da ‘yanci.
Ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta riga ta kafa cibiyoyin gyaran masu shaye-shaye na maza da mata, tare da alƙawarin ci gaba da faɗaɗa ayyukan gyaran hali da dawo da waɗanda suka kamu da shaye-shaye cikin al’umma.
Dangane da Dokar Zartarwar da ya sanya wa hannu, Gwamna Abba ya ce za ta samar da ingantaccen tsarin doka da zai taimaka wajen tarwatsa ƙungiyoyin daba, dakile tashe-tashen hankula masu alaƙa da siyasa da kuma ƙarfafa ayyukan hukumomin tsaro wajen tabbatar da doka da oda a Kano.
Da yake jawabi bayan ƙaddamar da kwamitin, shugaban kwamitin, Barrista Muhuyi Magaji Rimingado, ya gode wa gwamnan bisa amincewar da ya nuna masa da sauran mambobin kwamitin.
Ya yi alƙawarin gudanar da aikin da aka ɗora musu cikin gaskiya, ƙwarewa da riƙon amana, ba tare da nuna son kai ko sassauci ba.
Muhuyi ya ce kwamitin zai yi aiki tare da hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, shugabannin addini, ƙungiyoyin fararen hula, cibiyoyin ilimi da shugabannin al’umma domin yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.
A ƙarshe, Gwamna Abba ya yi kira ga al’ummar Kano da su ba kwamitin haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai ga hukumomin tsaro, yana mai cewa yaƙi da shaye-shaye da daba ba aikin gwamnati kaɗai ba ne, illa haɗin kan kowa da kowa.
Ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa haɗa Dokar Zartarwar da ayyukan sabon kwamitin zai taimaka wajen rage laifukan da ke da alaƙa da miyagun ƙwayoyi, tare da samar da Jihar Kano mai zaman lafiya da tsaro.

