Wani rahoton ‘yansanda ya bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na manyan laifuka a Jihar Kano na da alaƙa da shan miyagun ƙwayoyi da fataucinsu, lamarin da ya nuna yadda matsalar ke da nasaba da rikice-rikicen daba da a yankin.
Rahoton sirri da aka samu ya nuna cewa shan miyagun ƙwayoyi ya zama babban abin da ke ƙarfafa ƙungiyoyin daba, waɗanda ke shiga rikice-rikicen tashin hankali, hare-haren makamai da faɗace-faɗacen titi a sassan jihar.
Rahotan, wanda rundunar ‘yansandan Jihar Kano ta tattara ƙarƙashin jagorancin kwamishinan ‘yansanda Ibrahim Adamu Bakori, ta nuna cewa an kama mutane 3,081 da ake zargi da manyan laifuka a shekarar 2025, inda da dama daga cikinsu ke da alaƙa da harkokin miyagun ƙwayoyi.
Rahoton ya bayyana halin da ake ciki a matsayin abin damuwa, inda cibiyoyin fataucin miyagun ƙwayoyi ke ci gaba da bunƙasa tare da ƙara ruruta laifukan tashin hankali da ke haddasa mace-mace, jikkata mutane da lalata dukiyoyi.
Sai dai rahoton ya yi gargaɗin cewa matsalar na iya ƙara tsananta idan ba a ɗauki mataki mai ƙarfi ba, yana mai cewa rashin ɗaukar mataki zai iya haifar da ƙarin ƙaruwar laifuka da barazana ga tsaron jama’a.
Bincike ya kuma nuna cewa ƙungiyoyin daba da ke da alaƙa da Fadan Daba na samun goyon baya daga hanyoyin rarraba miyagun ƙwayoyi, waɗanda ke samar musu da kuɗi da tallafi.
Domin shawo kan matsalar, ‘yan sanda sun ba da shawarar kafa rundunar haɗin gwiwa da za ta haɗa da ‘yan sanda, hukumar NDLEA, ƙungiyoyin sa-kai da sauran hukumomin tsaro domin gano masu laifi, kama su tare da gurfanar da su a gaban kotu, da kuma lalata hanyoyin fataucin miyagun ƙwayoyi.
Rahoton ya jaddada cewa amfani da ƙarfi kaɗai ba zai wadatar ba, inda ya buƙaci a haɗa da shirye-shiryen wayar da kai da kuma gyaran halayen masu shaye-shaye. Haka kuma an ba da shawarar gudanar da yaƙin neman wayar da kai a faɗin jihar, tare da haɗa kan sarakunan gargajiya, malamai da shugabannin al’umma.

