Wani jirgin sojin Amurka ya yi hatsari a Iraƙi, kamar yadda rundunar sojin Amurka ta tabbatar.
Jirgin sojin na KC-135 ya faɗo ne bayan wani “hatsarin” da ya shafi wasu jirage biyu.
Rundunar sojin Amurka ta ce “ana ci gaba da aikin ceto” a yammacin Iraƙi – abin da sojoji suka ce ya faru ne a “yankin da ba na maƙiya ba.”
“Lamarin ba ya faru ba ne a yankin da ake yaƙi ko kuma musayar wuta,” in ji sanarwar.
Jirgi na biyu da lamarin ya shafa ya sauka lafiya, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Babu dai tabbas kan adadin mutanen da ke cikin jirgin da kuma makomarsu.
Sannan ba a san dalilin da ya haddasa hatsarin jirgin ba, da kuma asalin wurin da hatsarin ya faru.
Ana hasashen jirgin sojin wanda ke ba jiragen yaki na Amurka mai ya yi taho mu gama ne da wani jirgin a sararin samaniya.
Irin jiragen masu tankar mai na taka rawa sosai a yaƙi, inda jiragen yaƙi da masu kai harin bama-bamai ke dogaro da su musamman idan har sai sun yi dogon zango kafin inda za su kai hari.
Rundunar sojin Amurka ta ce lamarin ya faru ne a Iraƙi amma ba a san tazarar da ke tsakanin wurin da makwabciyarta Iran ba.
Wannan na zuwa bayan rundunar sojin Faransa ta ce wani harin jirgi marar matuki ya raunata sojojinta shida a yankin Kurdawa na Iraƙi a ranar Alhamis.
An kai masu hari ne a lokacin da suke atisaye tare da dakarun Iraƙi, kamar yadda rahotanni suka nuna .

