Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Farashin litar man fetur ya zarce naira dubu 1 a sassan Najeriya
Afrika

Farashin litar man fetur ya zarce naira dubu 1 a sassan Najeriya

March 9, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
FB IMG 1773006543246

Daga wannan Lahadi farashin man fetur a birnin Legas na Najeriya ya yi tashin gwauron zabi, inda yanzu ya kai tsakanin ₦1,040 zuwa ₦1,080 a kowace lita a gidajen mai daban-daban.

Wannan ƙarin ya biyo bayan hauhawar farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya, sakamakon faɗaɗa yaƙi tsakanin kasashen Amurka, Isra’ila, da kuma Iran wanda ke barazana ga harkar man fetur.

Tashin hankali a yankin Gabas Ta Tsakiya, wanda ya haɗa da hare-hare kan jagororin Iran da cibiyoyin man fetur, ya sanya farashin ɗanyen mai na Brent ya kusanci dala $90 zuwa $100 a kowace ganga.

Wannan lamari ya jefa kasuwannin duniya cikin ɗar-ɗar, wanda ke shafar kasashe masu shigo da tataccen mai kamar Najeriya kai-tsaye.

A nan gida, matatun mai sun fara daidaita farashinsu don dacewa da halin da ake ciki, inda matatar man Dangote ta kara farashi daga ₦874 zuwa ₦995 a cikin kwanaki huɗu kacal.

Kamfanin ya bayyana cewa tsadar danyen mai da ake sayowa don tacewa ita ce babban dalilin da ya tilasta wannan karin farashin.

Gidajen man na kamfanin NNPC Retail da ke sassan Legas su ma sun sauya farashinsu zuwa kusan ₦1,040 a kowace lita, daga tsohon farashin da yake kusan ₦993.

Sauran gidajen mai masu zaman kansu irinsu Techno Oil, Mobil, da MRS su ma suna sayar da man a kan farashi daban-daban da ya kama daga ₦1,050 har zuwa kusan ₦1,100 a wasu wuraren.

Masana tattalin arziki sun yi gargadin cewa idan har rikicin Iran ya kai ga toshe mashigin ruwa na Hormuz, farashin ɗanyen mai na iya haura dala $120 zuwa $130 akan kowace ganga.

Idan hakan ta faru, akwai yiwuwar farashin fetur a Najeriya ya kai ₦1,200 ko fiye da haka, wanda zai kara tsananta halin rayuwa ga talaka.

Wannan hauhawar farashin man tuni ya fara shafar farashin abinci da sufuri a fadin kasar, yayin da direbobin motocin haya ke korafin tsadar man. Jama’a na ci gaba da sanya ido kan yadda diflomasiyyar duniya za ta karkata don ganin ko za a samu saukin wannan rikici da ya addabi tattalin arzikin duniya.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Sojojin UAE biyu sun mutu a hatsarin jirgin sama – Ma’aikatar tsaro

March 10, 2026

Mojtaba Khamenei Ya Gaji Mahaifinsa A Matsayin Jagoran Addinin Iran

March 9, 2026

Mutanen da ake hasashen za su maye gurbin Mataimakin Gwamnan Kano

March 7, 2026

Yakin Amurka/Isra’ila da Iran: Lallai da ni za a zaɓi sabon shugaba a Iran – Trump

March 6, 2026

Majalisar Dokokin Kano ta fara yunƙurin tsige mataimakin Gwamna

March 6, 2026

Gwamnatin Jigawa Ta Tsige Alƙalin Kotun Musulunci Kan Rashawa

March 4, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Bincike Na Musamman

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

By WafsymMarch 9, 2026

‎Rundunar Kano Neighbourhood Watch Security Corps, wadda gwamnatin Jihar Kano ta kafa domin tallafawa hukumomin…

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026

KANO: Farashin Kayan Masarufi Ya Yi Tashin Gwauron Zabi Gabanin Shigowar Azumin Ramadan ‎ ‎

February 12, 2026

‎“Ya Kamata ‘Yan Jaridu Su Riƙa Nuna Tausayi, Hikima Da Mutunta Jinƙan Ɗan Adam wajen ɗauko labarai ‎ ‎ ‎—Comrade Abbas Ibrahim

January 21, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.