Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Mutanen da ake hasashen za su maye gurbin Mataimakin Gwamnan Kano
Afrika

Mutanen da ake hasashen za su maye gurbin Mataimakin Gwamnan Kano

March 7, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
25489720 1884 11f1 aff7 a32b6621d3cc.jpg

Majalisar Dokokin Jihar Kano a ranar Alhamis ta ƙaddamar da matakan tsige Mataimakin Gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, bisa zargin aikata ba daidai ba, amfani da iko ta hanyar da ba ta dace ba da kuma cin amanar ƙasa.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini Dala ne ya gabatar da takardar sanarwar tsigewar a zauren majalisar, inda ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne daidai da sashe na 188 na Kundin Tsarin Mulkin Jamhuriyar Tarayyar Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa gyara).

Yakin Amurka/Isra’ila da Iran: Lallai da ni za a zaɓi sabon shugaba a Iran – Trump

A cewarsa, takardar tsigewar ta ƙunshi zarge-zarge da dama da suka shafi lokacin da Gwarzo yake riƙe da muƙamin Kwamishinan ƙananan Hukumomi tsakanin 2023 zuwa 2024, da kuma matsayinsa na yanzu a matsayin mataimakin Gwamna.

Wadanda ake hasashen za su maye gurbin Mataimakin Gwamnan

Tun bayan ficewar Gwamnan Jihar daga jam’iyya a watan da ya gabata, ba a cika ganinsa a tarukan gwamnati tare da mataimakinsa ba. Akasin haka, shi kuwa Abdussalam ya kasance yana halartar tarukan Jam’iyyar NNPP tare da jagoran jam’iyyar na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso.

Tuni dai alamun yiwuwar samun wanda zai maye gurbin Abdussalam suka fara ƙarfi.

Daga cikin manyan mutanen da ake sa ran za su gaje shi idan har aka tsige shi, akwai ɗan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2023, Murtala Sule Garo; Da tsohon ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a zaɓen 2015, Salihu Sagir Takai; har ma da Shugaban Majalisar Dokokin jihar na yanzu, Jibril Isma’il Falgore.

Wasu masu lura da al’amuran siyasa na ganin cewa Kwankwaso na iya tsayar da Gwarzo takara domin ya ƙalubalanci Gwamna Yusuf a zaɓen 2027, idan har shirin tsige shi ɗin ya yi nasara.

Zargin karkatar da kuɗaɗe

Dala ya yi zargin cewa sa’ilin da yake riƙe da muƙamin Kwamishinan Karamar Hukuma kuma yake kula da harkokin ƙananan hukumomi 44 na jihar, mataimakin Gwamnan ya shiga hannu wajen karkatar da kuɗaɗen da aka ware don ayyukan ƙananan hukumomin.

Tsakanin watan Yunin 2023 zuwa Janairun 2024, ana zargin Abdussalam da karɓar cin hanci na Naira miliyan 1.5 daga kowace ƙaramar hukuma cikin guda 44 a kowane wata.

Wannan tsari, a cewar shugaban masu rinjaye, ya kai Naira miliyan 66 a kowane wata har tsawon wata bakwai, wanda jimillar kuɗin ya kama Naira miliyan 462.

Ya ƙara da zargin cewa, tsakanin watan Fabrairu zuwa Yulin 2024, Abdussalam ya karɓi wasu ƙarin kuɗaɗe daga ƙananan hukumomin a ƙarƙashin sunan gudanar da wasu ayyuka na musamman. Waɗannan kudade, in ji shi, sun kai Naira miliyan 3.255 a kowane wata daga kowace ƙaramar hukuma, wanda hakan ya kawo jimillar kuɗi kusan Naira miliyan 726 a cikin wata shida.

“Wadannan kuɗaɗen da ake zargin an biya su sun zama wani babban cin amana ne kuma sun saɓa wa ƙa’idojin gaskiya da riƙon amana da ake tsammani daga babban jami’in gwamnati,” in ji Dala a gaban majalisar.

Haka kuma, takardar tsigewar ta zargi mataimakin gwamnan da cin zarafin ofis. Dala ya yi iƙirarin cewa Gwarzo ya yi amfani da matsayinsa na Kwamishina wajen bada umarnin biyan Naira miliyan 10 daga kowace ƙaramar hukuma cikin guda 44 ga kamfanin NovoMed Pharmaceuticals Limited.

 

 

AMINIYA

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Sojojin UAE biyu sun mutu a hatsarin jirgin sama – Ma’aikatar tsaro

March 10, 2026

Mojtaba Khamenei Ya Gaji Mahaifinsa A Matsayin Jagoran Addinin Iran

March 9, 2026

Farashin litar man fetur ya zarce naira dubu 1 a sassan Najeriya

March 9, 2026

Yakin Amurka/Isra’ila da Iran: Lallai da ni za a zaɓi sabon shugaba a Iran – Trump

March 6, 2026

Majalisar Dokokin Kano ta fara yunƙurin tsige mataimakin Gwamna

March 6, 2026

Gwamnatin Jigawa Ta Tsige Alƙalin Kotun Musulunci Kan Rashawa

March 4, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Bincike Na Musamman

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

By WafsymMarch 9, 2026

‎Rundunar Kano Neighbourhood Watch Security Corps, wadda gwamnatin Jihar Kano ta kafa domin tallafawa hukumomin…

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026

KANO: Farashin Kayan Masarufi Ya Yi Tashin Gwauron Zabi Gabanin Shigowar Azumin Ramadan ‎ ‎

February 12, 2026

‎“Ya Kamata ‘Yan Jaridu Su Riƙa Nuna Tausayi, Hikima Da Mutunta Jinƙan Ɗan Adam wajen ɗauko labarai ‎ ‎ ‎—Comrade Abbas Ibrahim

January 21, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.