Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa yana bukatar a saka Amurka cikin tsarin zaben sabon shugaban Iran.
Trump ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da kafar yada labarai ta Axios ranar Alhamis, kwanaki biyar bayan kashe jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, a wani hari da Amurka da Isra’ila suka kai kan gidansa a Tehran.
Majalisar Dokokin Kano ta fara yunƙurin tsige mataimakin Gwamna
A cewar Trump, Iran na bata lokacinta idan ta yi kokarin nada sabon jagora ba tare da sa hannun Amurka ba.
Ya kuma bayyana cewa Mojtaba Khamenei, ɗan marigayi Ali Khamenei wanda ake ganin zai iya gaje shi, ba zabin da zai amince da shi ba.
Trump ya bayyana shi a matsayin mutum mara karfi, yana mai cewa:
“Dan Khamenei ba zabin da zan amince da shi ba. Muna son wanda zai kawo zaman lafiya da hadin kai a Iran.”
Ya kara da cewa dole ne shi kansa ya shiga cikin tsarin zaben sabon shugaban, yana mai kwatanta lamarin da yadda Amurka ta shiga cikin sauyin shugabanci a Venezuela.
Trump ya kuma ce ba zai amince da duk wani sabon shugaban Iran da zai ci gaba da manufofin gwamnatin da ta gabata ba.
A cewarsa, idan hakan ta faru, za a iya sake samun rikici tsakanin Amurka da Iran cikin shekaru biyar masu zuwa.
Tun da farko, Trump ya ce mafi munin sakamakon yakin da ake yi yanzu shi ne idan wani shugaba mai tsattsauran ra’ayi kamar marigayi Khamenei ya karbi mulki.
Ya kuma bayyana cewa wasu daga cikin mutanen da Amurka ta yi tunanin za su iya jagorantar Iran sun mutu a hare-haren farko da aka kai.
Kalaman Trump na zuwa ne yayin da yakin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Iran ke ci gaba, inda rahotanni suka nuna cewa sama da Iraniyawa 1,000 sun mutu, yayin da sojojin Amurka shida da mutane 11 a Isra’ila suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren Iran.zaɓi sabon shugaba a Iran – Trump.
Premium times

