Shugabannin jami’ar Jihar Osun (UNIOSUN) sun yi kira da suna kamfanin Sally Tibbot Ltd cewar ya rubuta takardar neman a yafe mata a kan rahoton binciken yadda aka biya albashi inda har aka gano da ‘’akwai ma’aikatan Bogi da suka kai 250 .”
Da yake ganawa da manema labarai ranar Asabar, a Osogbo, mataimakin Shugaban jami’ar Farfesa.Clement Adebooye, ya yi barazanar cewar Jami’ar na iya ɗaukar matakin shari’a domin tana son abi mata ba’asin da ya kai ga sa yi mata irin wannan cin fuskar, matuƙar shi kamfanin yaƙi lashe aman da ya yi na zarginsu da hakan ba cewar akwai ma’aikatan Bogin.
Adebooye yace duk da yake ya shiga cikin lamarin na tantancewar amma duk da hakan sai da sunansa ya fito daga cikin jerin sunayen na ma’aikatanda ake zargin na Bogi ne a rahoton binciken da aka fitar bayan kammala shi binciken.
Kamar yadda ya ce, ma’aikata 249 ne aka cena Bogi ne lamarin da ya ce shin ne ya ƙara jefa lalata mutuncin Jami’ar a idanin al’umma.
“Masu kula da harkokin Jami’ar da kuma Shugabanninta sun yi marahoton kallon cewar wani al’amari ne neman da ake yi a ɓata mata suna, ba ayi bane yadda ya dace, an kuma so ne a ɓata sunanta kan irin yadda aka ɗauke da darja kamar yadda ya ce,”.
Mataimakin Shugaban jami’ar ya ce abinda ya lura da wanda aka damƙawa aikin shi ne bai saba da irin yadda lamarin ma’aikatan Jami’a yake,wato kamar ma’aikata kamar waɗanda su iyakarsu shekara shida ne zuwa bakwai, sai masu aukar hutu ma’aikatan wurin ne saboda su ƙaro karatu, wasu Malaman Jami’oi da ake yin hayarsu su zo domin karntarwa,sai kuwa wasu Malaman da ake basu damar yin bincike waɗanda na wucin gadi ne, daga koyawa har ma da na ɓangaren da ya shafi tafiyar da ita Jami’ar, su ma ana basu irin wannan damar ta hutun ana biyan su ne
Ya bayyana da akwai ma’aikata da yawa waɗanda aka amince da su tafi hutu domin ƙaro karatu, amma sai ga shi su ma an sa su cikin ajin ma’aikatan Bogi.
“Sai dai kuma maganar ma’aikatan Bogi 250 ( da aka ce suna nan) hakan ya ƙara nunwa a fili irin Cece- kucen da ake yi na Sally Tibbot ta maida hankali ne kan maganar dawowarta wurin, maimaikon ma tunanin da ake yi na akwai alamun gaskiya akan shi aikin binciken na ma’aikata da aka yi.
“Bugu da ƙari kuma Jami’ar kamar yadda ta ce lamarin ya ɗaure mata kai matuƙa kana irin abubuwan da aka yi amfani d a su wajen gano su ma’aikatan na Bogi, musamman ma, a lokacin da aka yi shi binciken na gano hakan kowa ya zo da kan shi ne an kuma gan shi kamar yadda ya jaddada,”.
Jami’ar ta ƙara jaddada buƙatarta ta a nemi gafara daga gare ta, bata haƙuri da kuma su ma’aikatan da abin ya shafa, idan kuma an ƙi ɗaukar matakin zai sa a ɗauki ko yanke shawarar kai al’amarin zuwa kotu.
Kamar yadda yace “Muna sa ran a rubuta mana takarda ta bamu haƙuri kan laifin da aka yi mana daga ita hukuma ga ita makarantar wato Jami’ar da kuma ma’aikatan da abin ya shafa daga ita Sally Tibbot. Mataimakin Shugaban Jami’ar da manyan Farfesoshin sun yi matuƙar damuwa akan irin kiraye- kirayen wayar da ake yi masu,saƙonni da kuma wasiƙu/ takardu daga cikin gida da kuma hukumomin ƙasashen waje dangane da yadda binciken yawan ma’aikatan Jami’ar Jihar Osun ya kasance.Muna iya zuwa kotu domin muma a bi mana hakkinmu,”cewar Adebooye.
Matsalar ta faro asali ne lokacin da aka yi bin diddiƙin dangane sanin ko ma’aikata nawa ake da su wanda aka yi tsakanin watannin Mayu da Yuni na 2023, wanda wani kamfani da ake kira ya yi ma gwamnatin Jihar Osun.
Shi dai Bakrin-Ottun tun da farko ne ya yi zargin cewar gwamnatin Jihar ta gaza ko ta kasa caukar mataki bayan rahoton binciken da aka yi ya gano da akwai da akwai ma’aikatan Bogi da suka kai 15,000 da kuma waɗanda suka yi ritaya a cikin bayanan kuɗaɗen biyan albashi.
Sai dai kuma gwamnatin Jihar Osun, ta hannun Kwamishina yaɗa labarai da wayar da kan al’umma, Kolapo Alimi, ya zargi shi Kamfanin cewa bayanan da ya bada akan ma’aikatan Bogi na Jihar abin bai kai haka bal yayi hakan ne domin ladar da za’a ba shi ta kasance mai yawa.
Yayin da jam’iyyar APC rashen Jihar na (APC) Osun ya yi kira da hukumomin hana yin al’amuran da suka shafi cin amana ta hanyar karɓar rashawa da cin hanci (ICPC) da (EFCC) su yi binciken domin gano yadda har aka samo bambance bambancen a a takardun biyan albashi.
Mai magana da yawun jam’iyyar APC Kola Olabisi cewa binciken ne kaɗai zai iya gano gaskiyar lamarin na yadda abin ya faru da kuma su wanene ke da laifi.
Yatib da shi ma yake tofa albarkacin bakinsa Shugaban jam’iyyar (PDP), na Jihar Sunday Bisi, ya zargi Ƴan adawa ne suke kare shi kamfanin da yayi bincike ya kuma gano mutanen Bogi da suka kai yawan 250 da har hakan yasa ake ta yin maganganu kan lamarin, kuwa lokacin da ake yin binciken an gano akwai abubuwan da ba dai dai suke ba.
Don haka abinda ya fi dacewa ayi shi ne maida hankali kan yin gyara irin waɗanda gwamnatin Jihar take amfani da su.
LEADSHIP

