Hukumar Kwastam ta Ƙasa a yankin Sakkwato da Zamfara ta kama miyagun ƙwayoyi da darajarsu ta kai naira miliyan 99.9, sannan ta miƙa su ga Hukumar NDLEA a Sakkwato.
Kwanturulan yankin, Aliyu Musa Ndako ne, ya miƙa ƙwayoyin ga kwamandan rundunar NDLEA na jihar.
Dakarun Soji Sun Daƙile Harin Lakurawa Kan Wata Kasuwa a Kebbi
Ndako ya ce jami’an Kwastam sun cafke kayayyakin ne bayan wani da ba a san ko wane ne bar su a ƙauyen Maidoro da ke kan titin Sakkwato zuwa Illela.
Ya ce miyagun ƙwayoyin sun haɗa da kwalaye 182 na maganin tari na CST mai ɗauke da sinadarin kodin, da kuma ƙwayoyin NASACAM Piroxicam, waɗanda ake zargin an shigo da su cikin ƙasar nan ta haramtacciyar hanya.
Ya ƙara da cewa kamen ya biyo bayan umarnin shugaban Hukumar Kwastam ta Ƙasa, Bashir Adewale Adeniyi, na a miƙa duk haramtattun ƙwayoyi ga NDLEA domin ci gaba da bincike.

