Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Amurka Ta Buƙaci Najeriya Ta Katse Cinikin makamai da Rasha
Afrika

Amurka Ta Buƙaci Najeriya Ta Katse Cinikin makamai da Rasha

February 25, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
tinubu and trump 750x536 1

Wasu ’yan majalisar dokokin Amurka ƙarƙashin jagorancin ɗan majalisa Riley Moore, sun miƙa wa Fadar White House wani rahoto na musamman kan zargin tsananta wa Kiristoci a Najeriya, inda suka jaddada buƙatar a sanyawa ƙasar takunkumi.

Rahoton ya ba da shawarar sanyawa da kuma jaddada takunkumin hana biza ga duk mutumin da aka samu da hannu wajen tauye hakkin addini ko kisan Kiristoci a Najeriya.

Dakarun Soji Sun Daƙile Harin Lakurawa Kan Wata Kasuwa a Kebbi

Wannan rahoto ya biyo bayan bincike ne da Shugaba Trump ya umarci Riley Moore da Tom Cole su jagoranta, inda suka bayyana Najeriya a matsayin kasa mafi hadari a duniya ga Kiristoci.

‘Yan majalisar sun buƙaci gwamnatin Amurka ta yi nazarin dakatar da shigo da naman shanu da sauran kayayyaki daga Najeriya don matsa lamba ga makiyaya masu ɗauke da makami su ajiye makamansu.

Rahoton ya goyi bayan matakin Shugaba Donald Trump na sake sanya Najeriya a cikin jerin ƙasashen da ke da matsalar ƙuntatawa kirstoci.

‘Yan majalisar sun buƙaci Najeriya ta soke dokokin shari’a da na ɓatanci waɗanda suka ce ana amfani da su wajen gallaza wa Kiristoci.

Sun kuma ba da shawarar dakatar da wasu tallafin kudi da Amurka ke ba wa Najeriya har sai gwamnatin ƙasar ta ɗauki matakan zahiri na dakatar da tashe-tashen hankula.

Tawagar ta Riley Moore ta kuma bayar da shawarar cewa Najeriya ta daina sayen makaman Rasha, maimakon haka ta sayi na Amurka a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar tsaro ta haɗin gwiwa.

Gwamnatin Najeriya dai ta sha musanta waɗannan zarge-zarge, tana mai cewa rikice-rikicen da ke faruwa a ƙasar basu da alaƙa da addini, illa ‘yan ta’adda da ke addabar mabiya mabanbantan addinai.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Rikicin ACF: Lokaci Ya Yi Na Rushe Tsohon Tsari Da Yin Garambawul —Abbas Ibrahim 

May 12, 2026

Za mu mayar da martani kan harin da aka kai wa jirgin ruwanmu – Koriya ta Kudu

May 11, 2026

Dalilin da ya sa na maida akwatin zaɓena Abuja – Pantami

May 11, 2026

Dangote na shirin gina matatar mai a ƙasar Kenya

May 11, 2026

Samar da Aminci, Shi Ne Farko — Dole a Kawar Da Siyasar Dauka Makamai Daga Fagen Siyasar Kano

May 5, 2026

Pantami ya yi watsi da tsarin maslaha bayan kin daukar shi a matsayin dan takarar gwamnan Gombe

May 3, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda

By WafsymApril 25, 2026

Wani rahoton ‘yansanda ya bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na manyan laifuka…

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

April 2, 2026

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.