Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Ƴan Bindiga sun sa harajin miliyan 100 ga malaman da ke son yin wa’azi a Kebbi
Afrika

Ƴan Bindiga sun sa harajin miliyan 100 ga malaman da ke son yin wa’azi a Kebbi

February 23, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
pztktkpTURBXy8yNTQxNmNmNzMyMDY2OTNjYjJmZDE4YjBhNjQ3Yzg4YS5qcGeSlQMAAM0CCM0BJZMFzQKAzQFA

A wani yanayi da matsalolin tsaro ke ci gaba da ta’azzara a jihohin yankin arewa maso yammacin Najeriya, ƴanbindiga sun buƙaci malamai su biya harajin naira miliyan 100 gabanin samun damar yin wa’azi a wani yanki na jihar Kebbi.

Al’umma sun shiga tashin hankali a garin Utouno na ƙaramar hukumar Ngaski da ke jihar ta Kebbi guda cikin jihohin da ke fama da matsalar tsaron, bayan samun umarnin biyan wannan kuɗi gabanin gudanar da wa’azi ko kuma Tafsiri cikin watan da muke na azumin Ramadana.

Shugaba Tinubu ya taya murna ga waɗanda suka lashe zaɓukan Abuja, Kano da Rivers

Wasu majiyoyi sun ce ƴan ta’addan sun aika ta wasiƙa da shugabannin gargajiya na yanki har ma da malumman da ke gudanar da wa’azin inda suka nemi su biya tsabar kuɗin har naira miliyan 100 gabanin samun damar yin wa’azin.

Wasiƙar ƴanbindigan ta yi gargaɗin fuskantar hukunci ga duk waɗanda suka bijirewa biyan harajin yin wa’azin.

Wannan umarni na ƴanbindigar na zuwa ne a wani yanayi da ake ganin ta’azzarar hare-haren ƴan ta’addan da ake kira Lakurawa waɗanda suka kai hari ƙaramar hukumar Kangiwa tare da kashe mutane 33.

Mazaunin wani gari da suka samu wannan wasiƙa daga ƴanbindigar wanda kuma ya nemi a sakaya sunanshi ya ce hankalin jama’a ya tashi matuƙa a yankinsu, wanda ya sanya hatta malamai shiga fargabar iya gudanar da wa’azin.

Tuni dai Gwamnan jihar Nasir Idris ya yi umarnin aikewa da ƙarin dakaru zuwa yankin don bayar da cikakkiyar kariya ga jama’a.

Bisa al’ada watan Ramadana lokaci ne da akan gudanar da karatuttukan tare da mabanbatan wa’azi iri iri don sake kusanta jama’a da mahaliccinsu.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Gwamnan Kano ya sauke shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Abdullahi Musa daga mukaminsa

March 11, 2026

Sojojin UAE biyu sun mutu a hatsarin jirgin sama – Ma’aikatar tsaro

March 10, 2026

Mojtaba Khamenei Ya Gaji Mahaifinsa A Matsayin Jagoran Addinin Iran

March 9, 2026

Farashin litar man fetur ya zarce naira dubu 1 a sassan Najeriya

March 9, 2026

Mutanen da ake hasashen za su maye gurbin Mataimakin Gwamnan Kano

March 7, 2026

Yakin Amurka/Isra’ila da Iran: Lallai da ni za a zaɓi sabon shugaba a Iran – Trump

March 6, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Bincike Na Musamman

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

By WafsymMarch 11, 2026

Sabbin matakan da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dauka na fara shirin tsige Mataimakin Gwamna,…

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026

KANO: Farashin Kayan Masarufi Ya Yi Tashin Gwauron Zabi Gabanin Shigowar Azumin Ramadan ‎ ‎

February 12, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.