Hukumar ICPC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya ta ƙaddamar da mataki na takwas na shirin bibiyar ayyukan mazaɓu da na sashen zartarwa a Jihar Katsina, inda ake sa ido kan jimillar ayyuka 39 da kuɗin su ya kai naira biliyan 13.5 a yankunan sanatoci da mazaɓun tarayya na jihar.
A cewar hukumar, tawagar bibiyar ayyukan ta haɗa da manyan jami’ai daga hedikwata da ofishin Katsina.
Kotu Ta Ci Tarar Ƴansanda Naira Miliyan 30 Kan Ayyana Neman Sowore Ruwa A Jallo
Hukumar ta ce ana gudanar da aikin ne tare da haɗin gwiwar Nigerian Institute of Quantity Surveyors da kafafen yaɗa labarai domin tabbatar da inganci, amfani da kuɗi yadda ya dace, da bin ƙa’idojin ayyuka.
Tuni an duba ayyukan cibiyoyin lafiya a birnin Katsina, hanyoyi a Funtua da Kankia, da ayyukan samar da ruwa a Kurfi, Dutsin-Ma, Mashi da Dutsi. Haka kuma an bibiyi ayyukan makarantu a Ƙafur, Sandamu, Daura da Mai’Adua, tare da fitilun kan tituna na hasken rana da shirye-shiryen tallafa wa al’umma.
Hukumar ta ce shirin na gudana ƙarqashin kulawar daraktan ayyuka, Mr Ludam S. Samuel, a wani yunƙuri na ƙara haɓaka gaskiya da riƙon amana a ayyukan gwamnati.
Blueprint

