Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Jami’an Ƴansanda 5,000 Ake Sa Ran Za Su Yi Ritaya A Shekarar 2026
Babban Labari

Jami’an Ƴansanda 5,000 Ake Sa Ran Za Su Yi Ritaya A Shekarar 2026

February 5, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
911213ac e0cb 41c5 a6ef 08667832d487.png
911213ac e0cb 41c5 a6ef 08667832d487.png

Akalla jami’an rundunar ’yansandan Nijeriya 5,000 ake sa ran za su yi ritaya a shekarar 2026, in ji Mataimakin Kwamishinan ’Yansanda mai kula da fansho a shalƙwatar NPF, DCP Sani Doki Yusuf.

Yusuf ya bayyana hakan ne a Kano yayin taron horaswa na yankin Arewa maso Yamma ga jami’an da ke shirin ritaya, wanda NPF Pensions Limited ta shirya. Ya ce taron na da nufin wayar da kai kan muhimmancin cika takardun fansho yadda ya kamata domin kauce wa jinkiri wajen biyan haƙƙoƙi.

Jami’an Ƴansanda 5,000 Ake Sa Ran Za Su Yi Ritaya A Shekarar 2026

Ya ce matsalolin da ake fuskanta a biyan fansho sun fi shafar kurakurai a bayanan sirri, musamman bambancin suna da rashin daidaiton takardu, inda hukumar ke kai ziyara rundunoni domin gyara irin waɗannan matsaloli.

A cewarsa, NPF Pensions ta biya jimillar Naira biliyan 97.5 ga tsofaffin jami’ai 30,370 tun bayan kafuwarta, tare da biyan Naira biliyan 39.57 ga ’yan uwan jami’an da suka rasu 8,847. Haka kuma, tsofaffin jami’ai 25,572 na karɓar fansho na wata-wata sama da Naira biliyan 1.56.

Haka zalika, Darakta a Hukumar Fanshon ’Yansanda kuma Jami’ar Inshora ta Rundunar, ACP Lydia Ameh, ta ce jinkirin biyan fansho ya ragu matuƙa, inda ta jaddada cewa jami’an da suka cika takardunsu yadda ya dace na iya karɓar haƙƙinsu cikin kwanaki uku zuwa biyar na aiki.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Gwamna Abba Ya Kaddamar da Kwamitin Yaƙi da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, Ya Sanya Hannu Kan Dokar Daba A Kano

July 22, 2026

“Rikicin Shaidar Zama Ɗan Ƙasa a Jos North Ya Ɗauki Sabon Salo, Sarakunan Gargajiya Sun Nemi Shiga Cikin Shari’a.”

July 11, 2026

Sarkin Gaya: Mallakar Katin Zaɓe Shi Ne Ginshiƙin Zaɓen Shugabanni Nagari

July 3, 2026

Sahihin ‎Labari Ke Tabbatar Da Amincewar Jama’a, Ba Gaggawar Wallafa Ba- Shugaban NUJ

July 1, 2026

NWUK Expels 34 Students Over Examination Malpractice

June 30, 2026

Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Ƙara Wa NDLEA Motoci Don Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ‎

June 29, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Ƙara Wa NDLEA Motoci Don Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ‎

June 29, 20267

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda

By WafsymApril 25, 2026

Wani rahoton ‘yansanda ya bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na manyan laifuka…

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

April 2, 2026

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.