Ƙungiyar kare haƙƙin jama’a da sa ido kan kashe kuɗaɗen gwamnati, a Najeriya, SERAP ta shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, da Hukumar Kula da Lantarki ta Najeriya NBET, bisa zargin karkatar da Naira biliyan 128.
SERAP ta ce ta ɗauki wannan mataki ne bayan zarge-zargen da ke cikin rahoton Babban Mai Binciken Kuɗi na Tarayya da aka wallafa a watan Satumba na bara.
Ƙungiyar na neman kotu ta tilasta wa waɗanda ake ƙara su yi cikakken bayani kan kuɗin, tare da bayyana sunayen jami’ai ko kamfanonin da suka amfana da su.
A cewar SERAP, cin hanci da rashawa a ɓangaren wutar lantarki na ƙara jefa ’yan Nijeriya cikin duhu, inda ake fama da rushewar layin wuta da kuma biyan kuɗaɗen wuta masu tsada.
Sai dai har yanzu ba a sanya ranar sauraron ƙarar ba.

