Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Barau I Jibrin ya ce da zarar shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya mika masa gayyatar zama mataimakinsa a zaben shekarar 2027 da gudu zai karɓa.
Barau wanda ke ganawa da manema labarai a Abuja, ya ce a shirye yake ya sadaukar da kansa domin gudanar da duk wani aikin da shugaban ƙasar ya ba shi.
Sanatan wanda ya bayyana cewar ba ya buƙatar yin dogon jawabi dangane da lamarin a halin yanzu, ya ce lokaci bai yi ba da jama’a za su dinga tallata shi domin zama mataimakin shugaban ƙasa a zabe mai zuwa.
Barau ya ce bai ma san waɗannan ƙungiyoyin dake tallata shi ba, amma kuma ya buƙace su da su mayar da hankali wajen tallata ayyukan da shugaban ƙasa Tinubu ke yi da kuma goya masa baya.
Sanatan ya ce da zaran lokacin siyasa ya yi, za su sadaukar da lokutan su domin tinkarar duk wani kalubale, yayin da ya ƙara da cewar yanzu lokaci ne na mulki amma ba na siyasa ba.