Gwamnatin jihar kano ta ce ya kamata iyaye su dunga sanya idanu akan ƴaƴan su mata wajen sauke duk wani nauyi da yake kan su musamman yadda ƴaƴa mata suke da rauni da kuma wasu buƙatu da suke da su amma basa iya bayyanawa.
Babbar Daraktan Bincike da Adana bayanai ta gidan gwamnatin kano Hajiya Nana Asma’u Jibrin ce ta bayyana hakan a yau cikin wani ɓangare na ranar Al’adar mata ta duniya yayin bayar da tallafin kayan anfanin mata na yau da kullum ga ɗaliban makarantar First Lady dake nan kano domin ragewa iyaye nauyin siya musu.
Nana Asma’u Jibrin wanda ta samu wakilci Daraktan Tsare-tsare da bincike na ma’aikatar bincike da adana bayanai Abdulkarim Ibrahim Abubakar yace wannan tallafin an bayar da shi ne domin tallafawa yara mata da ƙunzugu domin wani lokacin kuɗin siyan yakan gagarar su.
Da take jawabi shugaban makarantar da First Lady Malama Atine Muhammad ta bayyana godiya bisa irin wannan gudummawar da aka bawa yaran makarantar tare da faɗakar da su yadda zasuyi anfani da shi.
Wakilin mu ya rawaito cewa Daraktar tasha alwashin tallafawa ƴaƴa mata a dukkannin ɓangarori na rayuwa domin gujewa daga faɗawa hali mara kyau.