Makusantan matashiyar nan da ta yi suna bayan jan hankalin gwamnatin jihar Sokoto kan matsalar tsaro sun tabbatar wa BBC cewa an tsince ta a wani daji na jihar Zamfara bayan batan-dabon da ta yi.
Tun ranar Talata ne aka bayar da rahoton ɓatan Hamdiyya Sidi Sharif, bayan ta fita domin zuwa kasuwa, lamarin da ya sanya ta kasa bayyana a zaman kotu kan shari’ar da ake mata a ranar Laraba a Sokoto.
A watannin baya ne dai gwamnatin jihar Sokoto ta shigar da matashiyar ƙara a gaban kotu, bisa zargin ta da aikata laifin tunzura tayar da zaune tsaye, shari’ar da har yanzu ake gudanar da ita.
A tattaunawarsa da BBC, lauyan da ke kare Hamdiyya, Abba Hikima ya ce yanzu haka tana wani asibiti da ke ƙaramar hukumar Bakura a jihar Zamfara “cikin mummunan yanayi.”