Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba kabir yusif, ya ce gwamnatinsa zata samar da ruwansha a masarautar Rano da garuruwan dake karamar hukumar ta hangar samar da matatar suwa dutsen Taluwaiwai dake karamar hukumar.
Gwamnan ya bayana hakan lokacin da ya Kai ziyarar aiki da yammacin yau Talata yana mai cewa “Yanzu haka gwamnati zata kawo kwararu dan yin bincike tare da samar da injinan yace ruwa na zamani” Cewar Gwamnan Kano.
Gwamnan ya kuma umarci Ma’aikatar ruwa ta jihar Kano ta gagauta bin hanyoyin da za a kammala aikin cikin kankanin lokaci.