Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) tare da Hukumar Hana Fataucin Mutane (NAPTIP) sun kafa wata rundunar jami’an su domin hada karfi tare wajen yaƙi da safarar miyagun kwayoyi da safarar mutane.
Wannan mataki ya fito ne a lokacin da Shugabar NAPTIP, Binta Lami Adamu Bello, ta kai ziyarar girmamawa ga Shugaban NDLEA, na Kasa Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa, mai ritaya a hedikwatar NDLEA dake Abuja, yau jumma’a 25 ga Afrilu, 2025.
A cikin jawabinsa, Marwa ya taya Binta Adamu Bello, murna bisa nadinta da shugaban Kasa Bola Ahamad Tunibu,yayi kuma ya yaba da yadda ta soma aiki da ƙwazo.
Ta cikin wata sanarwa da daraktan Yaɗa labarai da wayar daa kan jamma’a a hukumar Femi Baba Femi,Yafitar Ya bayyana cewa akwai alaƙa tsakanin safarar mutane da safarar miyagun kwayoyi, inda wasu daga cikin waɗanda ake safararsu ke zama masu ɗaukar kwayoyi ba tare da saninsu ba.
Sanarwar ta kara da cewa akwai bukatar haɗin gwiwa ta hanyar sanya hannu kan yarjejeniya (MoU) da za ta fayyace fannoni na aiki tare.
A nata bangaren, Shugabar yaki da safarar mutane da cin zarafin kananan Yara NAPTIP ta Kasa Binta Lami Adamu Bello, ta bayyana cewa akwai buƙatar haɗin kai sosai tsakanin hukumomin biyu domin toshe hanyoyin aikata laifukan, musamman ganin yadda ammfani da kananan Yara da Mata wajen safarar kwayoyi, sannan a kan yi musu allura ko a basu kwayoyi domin su kasance masu biyayya.
Ta kuma jaddada cewa laifukan biyu nafaruwa ne a iyakoki marasa tsaro, rashawa, talauci, da raunin hukumomi. Ta ce akwai buƙatar gina tsarin aiki na haɗin gwiwa wanda zai haɗa da bincike da musayar bayanan sirri, horas da ma’aikata tare, amfani da fasaha da bayanai, wayar da kai ga jama’a, da kuma yin garambawul ga dokoki.
Hukumomin sun amince da kafa shirin aiki na NDLEA da NAPTIP na lokaci gajere zuwa matsakaici, da gudanar da taron duba ayyuka sau ɗaya ko biyu a shekara, da kuma inganta haɗin gwiwa da ƙungiyoyi na ƙasa da ƙasa.