Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Sojojin Nijeriya sun sanar da kashe ɗan Bello Turji
Afrika

Sojojin Nijeriya sun sanar da kashe ɗan Bello Turji

January 20, 2025
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn

Sojojin Nijeriya sun tabbatar da kashe wasu makusantan kasurgumin ɓarayin daji Bello Turji  wanda suka addabi yankin Arewa maso yammacin Nijeriya.

Sanarwar da daraktan yada labaran hedkwatar tsaron Nijeriya, Manjo Janar Edward Buba ya fitar, ta ce sumamen da sojin ƙasar suka kai Shinkafi da Kagara da Fakai da Moriki da Maiwa da kuma Chindo sun yi sanadiyyar kashe gomman ‘yan ta’adda ciki har da ɗan Bello Turji da aka kashe a Fakai.

“Ƙarfin wutar da sojojin suka buɗe ya janyo mutuwar ‘yan ta’adda da yawa tare da lalata cibiyar adana kayayyakinsu. Harin ya kuma yi sanadiyyar ‘yanta wasu mutane da Bello Turji ya yi garkuwa da su. Kuma shugaban ‘yan ta’addan, Bello Turji, ya tsere ya bar ɗansa da sauran mayaƙansa,” in ji sanarwar.

Bello Turji yana cikin ɓarayin daji da suka yi ƙaurin-suna wajen garkuwa da mutane da kisa a arewa maso yammacin Nijeriya.

Sai dai a ƙarshen shekarar da ta gabata dai hedikwatar tsaron Nijeriya ta ce nan ba da jimawa ba za ta kashe Bello Turji.

Haka kuma a ƙarshen makon jiya ne rahotanni suka ce ɗan ta’addan yana tsere wa harin sojojin Nijeriya.

Kazalika sojin ƙasar sun lalata dabar wani ɗan ta’adda da ake kira Idi Malam a kan hanyar dajin Zango Kagara, in ji sanarwar.

“A lokacin arangamar, dakarun sun kashe ‘yan ta’adda uku tare da kama mutum uku da ake zargi da haɗa baki da su,” in ji Janar Buba.

Featured
Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Kwalejin Ilimi ta Isa Kaita dake Karamar Hukumar Dutsenma a Jihar Katsina ta tuna da Marigayi Isa Kaita

July 2, 2025

Da gudu zan karɓi tayin kujerar mataimakin shugaban Najeriya – Barau I Jibrin

June 26, 2025

Hatsaniyar data Faru a Karamar Hukumar Rano wadda ta kai ga Rasuwar DPO da wani mutum daya– ‘Yan sanda Sun Nemi Hadin kai don Dawo da Tsaro a Yankin

May 27, 2025

Babbar kotun shariar musulunci ta yankewa matashin nan Shafiu Abubakar hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin kashe wasu mutane

May 27, 2025

Hukumar tace fina-finai ta yi nasarar kama wasu na’urori da ake amfani dasu wajan buga hotunan batsa ga masu sana’ar maganin Gargajiya a Jahar Kano

May 26, 2025

Babbar Kotun Tarayya ta yi umarni ga Hukumar EFCC data cigaba da bincike kan filin Musabaka da ake zargin wasu a Jihar Kano sun siyar ba bisa ka’ida ba

May 23, 2025
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Kano

DALILAN DA YASA MUKAYI GWANJON TSAFFIN MOTOCIN DA MUKE GUDANAR DA AIKIN MU- NDLEA

By WafsymApril 13, 2025

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta bayana Dalilan yin Gwanjon…

Hukumar tace fina-finai ta haramtawa Usman Sojaboy da wasu mata biyu shiga harkokin Film ko waka a Kano

January 20, 2025

Madrid ko Barca: Wa zai lashe Spanish Super Cup?

January 12, 2025

Barca ta kara rashin nasarar ɗaukaka kara kan yi wa Olmo rijista

December 31, 2024
© 2025 WDN HAUSA
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.